Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, ya bayyana yadda ya fara jin labarin cewa an naɗa shi ya zama ɗan takarar da zai yi wa Buhari mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2015.
Ya ce ya na zaune a kununin gidajen Otal ɗin Panial Apartments, Abuja lokacin ya na nazarin ƙarar wani ɗan Majalisar Tarayya a Kotun Ƙoli, bayan ya canja sheƙa, sai aka kira shi, aka sanar da shi.
Osinbajo ya bada labarin a ranar Laraba, lokacin da ya gayyaci manema labaran da ke Fadar Shugaban Ƙasa su ka yi buɗe-baki tare da shi, a Gidan Mataimakin Shugaban Ƙasa da ke Aguda, cikin Fadar Shugaban Ƙasa, a Abuja.
“Ba zan manta ba a ranar 18 Ga Disamba, 2014, ina zaune wajen ƙarfe 1 na tsakar dare, Rauf Aregbesola ya kira ni. Ni a lokacin ina zaune a Rukunin Peniel Apartments, sai ya kira ni ya ce za su je Legas su ɗauko ni zuwa Abuja.
“Na ce masu ai ina Abuja, ina bibiyar wata shari’a a Kotun Ƙoli. Ya ce to da kyau, dama za mu zo mu ɗauke ka ne, saboda an zaɓe ka za ka tsaya wa Buhari ya takarar mataimakin shugaban ƙasa. Na ce masa to ku haka kawai ake naɗa mutum takara ne?” Inji Osinbajo.
Osinbajo ya ce bayan ya tashi daga kotu a ranar, ya koma masaukin sa. Ya ce bayan ya cire alkyabba da hular sa wato kayan lauya, “sai na kawo a rai na cewa wataƙila daya yau ba zan ƙara saka waɗannan kayan ba.”
Osinbajo ya ce a ranar ce Aregbesola da Ibikunle Amosun su ka kai shi ya gana da Buhari.
Ya ce ya shaida wa ‘yan jaridar haka ne domin ya sanar da su cewa rayuwar mutum kan iya canjawa cikin minti ɗaya.
Da ya ke masu barkwanci, Osinbajo ya shaida masu cewa “na gayyato ku ne domin ku bayar da ta ku gummawar.”
Da ya ke jawabi, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida Masu Ɗauko Labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, Ismaila Tsafe, ya ce sun daɗe su na aiki a fadar.
“Shugabanni da yawa sun same mu a nan,,kuma sun sun tafi, sun bar mu. Amma ba mu taɓa yin mu’amala da mai sauƙin kai kamar ka ba.”
Osinbajo, wanda zai kafsa zaɓen fidda gwani tare da Bola Tinubu, kwanan nan ya bayyana cewa ba zai iya cin amana ko butulce wa masu neman ya fito takara ba.
Ya ce dalili kenan ya amsa kiran su, ya fito takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2023.
Discussion about this post