Tsohon ministan Matasa Solomon Dalung ya fice daga jam’iyyar APC.
A sanarwar haka da yayi a wata takarda da ya mika wa gundumar sa Sabongida, ya ce kwatakwata jam’iyyar APC ta kauce daga irin manufofin da aka kafa ta akai. A dalilin haka ya hakura da jam’iyyar.
Sai dai kuma bai fadi jam’iyyar da zai koma ba.
Idan ba a manta ba Dalung ya taba bayyana cewa dole shugaba Buhari ya fito ya roki ‘yan Najeriya saboda karya alkawuran da ya dauka a lokacin kamfen a 2015.