Rashin bayar da gamsasshen bayani da hujjojin yadda za a sayo na’urorin da kuma tabbacin kamfanin da zai yi kwangilar, sun haddasa samar da jinkiri da kuma ƙin amincewar Majalisar Zartaswa a kwangilar sayen na’urorin hangen bam da ‘yan bindiga daga nesa, wadda Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya gabatar wa Majalisar Zartaswa kimanin watanni shida kafin ‘yan bindiga su kai mummunan farmaki kan jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin.
Wata takarda ko wasiƙar sirri da ta faɗo hannun wannan jarida ta nuna yadda Majalisar Zartaswa ta yi fatali da wata kwangila da Amaechi ya nemi bayarwa a ƙudundune.
Amaechi ya nemi Majalisar Zartaswa ta amince da kwangilar sayo na’urorin hange da tantance bam ko ‘yan bindiga daga nesa da aka yi niyya maƙala wa jiragen ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Majalisar Zartaswa ta ƙi amincewa ne saboda waɗansu dalilai da suka haɗa da:
Na farko dai Minista Amaechi ya kasa bayar da hujjar cewa kamfanin da zai bai wa kwangilar zai iya kawo kayayyakin.
Sannan Amaechi bai gamsar da Majalisar Zartaswa cewa kamfanin zai iya aikin maƙala na’urorin idan ya shigo da su ƙasar nan ba.
Dalili na uku, Majalisar Zartaswa ba ta amince da kwangilar ba, saboda aiki ne na maƙudan kuɗaɗe, har naira biliyan 3 da ɗoriya. Amma kamfanin da Amaechi ya yi niyyar bai wa kwangilar kwata-kwata bai taɓa yin irin wannan aikin ba.
Wani dalili kuma shi ne Minista Amaechi ya kasa gabatar wa Majalisar Zartaswa irin wasu ayyukan da kamfanin ya taɓa yi a baya, ballantana a gamsu cewa zai iya yin aikin samar da na’urorin.
Sannan kuma Amaechi bai kawo hujja daga wani wuri mai nuna cewa akwai inda aka yi amfani da irin na’urorin kuma a yanzu haka su na aiki sosai.
Wani dalili kuma shi ne, Majalisar Zartaswa ta gano cewa kamfanin da Amaechi ya bai wa kwangilar ɗan tagajan-tagajan ne, gaba ɗaya abin da ke cikin asusun kamfanin bai wuce naira miliyan 84.9 ba.
Sannan kuma kamfanin bai wuce shekaru uku da kafawa ba. Domin an kafa shi ne cikin 2019, sannan kuma ba shi da wata ƙwarewa ko gogewar yin irin ayyukan da Amaechi ya nemi a ba shi.
Wani dalilin kuma shi ne, Amaechi bai gabatar Da sunayen wasu kamfanonin da su ka nema aka hana su ba, ballantana a auna ta su ƙwarewar ko cancantar da kuma ta ɗan tagajan-tagajan ɗin kamfanin da Amaechi ya nemi bai wa kwangilar ba.
Wani dalilin kuma shi ne Amaechi bai yi wa kwangilar dalla-dalla ba. Kamata ya nuna cewa za a kashe kuɗaɗen a jirgin ƙasa masu zuwa garuruwa kaza da kaza. Shin iyakar masu zirga-zirga Abuja da Kaduna ne, ko kuwa har da na sauran garuruwa za a kashe wa kuɗaɗen? Duk Minista Amaechi bai yi haka ba.
Idan ba a manta ba, bayan kai hari kan jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, Amaechi ya bayyana cewa “da tun tuni an maƙala wa jiragen da ke zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna na’urorin, to da hakan bai faru ba.”
Sai dai kuma Amaechi bai wa duniya cewa shi ne ya haddasa sakacin ba, saboda ya bayar da kwangilar aikin samar da na’urorin a ƙudundune, kuma ga kamfanin da bai cancanta ba.
“An tsaya ana jayayya akan aikin samar da na’urorin na jiragen ‘drone’ kyamara mai-gani-har-hanji’. Ana buƙatar waɗannan na’urori domin ko daga nesa jirgi ya ke, za su nuna masa akwai matsala daidai wuri kaza da kaza. Idan wasu mutane ne ɗauke da makamai, duk na’urorin za su sanar.” Inji Amaechi.
Amma wasiƙar ƙin amincewa da ƙudundunen da Amaechi ya yi, ta faɗo hannun PREMIUM TIMES, wadda a Taron Majalisar Zartaswa na ranar 24 Ga Satumba, 2021, aka ƙi amincewa da kwangilar naira biliyan 3.7 ɗin da Ministan na Sufuri ya nemi bayarwa a sunƙaƙe.
Batutuwan da aka tattauna a wurin taron waɗanda aka rubuta, sun faɗo hannun wannan jarida. Sun nuna wani kamfani ne mai suna Mogjan Nigeria Limited wanda aka yi wa rajista a ranar 6 Ga Agusta, 2019 Amaechi ya so a bai wa Kwangilar.
Majiyar Fadar Shugaban Ƙasa ta shaida wa jaridar Punch cewa an ƙi amincewa da kwangilar saboda, “mun yi tantama da tababar ƙwarewar kamfanin, wanda bai ma fi shekaru biyu da kafuwa ba.
“Sannan kuma kamfanin bai taɓa yin aikin da ya kai naira biliyan 3.7 a baya ba. Bai kuma taɓa samar da na’urorin a wani wuri an tabbatar da ƙwarewar sa ba.”
A cikin wasiƙar dai an rubuta cewa Amaechi ya shaida wa Majalisar Zartaswa cewa Hukumar Tantance Kwangiloli ta Ƙasa (BPE) ce ta amince da kamfanin.
Tsakanin Tashar Jirgin Ƙasa ta Idu da ke Abuja da Tashar Jirgin Ƙasa ta Rigasa a Kaduna, tazarar kilomita 200 ce. A can ne Amaechi ke so a kashe zunzurutun naira biliyan 3.7.
Shi kan sa Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo wanda ya jagoranci Taron Majalisar Zartaswa a ranar, ya umarci Amaechi cewa ya na so ya san yadda na’urorin za su riƙa aiki idan ana amfani da su tukunna.
Shi kuwa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Ibrahim Gambari, ya nemi sanin shin a tsakanin jiragen Abuja da Kaduna kaɗai za a kashe kuɗaɗen ko har da na sauran garuruwa?
A nan ne Amaechi ya ce ai aikin na gwaji ne, idan ya yi sosai a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, to kuma sai a yi a sauran garuruwan da jiragen ƙasa ke zirga-zirga.