Sanata Uba Sani dake wakiltar Kaduna ta Tsakiya na daga cikin ƴan takaran da suka bayyana aniyarsu na maye gurbin gwamna Nasir El-Rufai a 2023.
A ganina babu wanda ya fi cancanta ta ɗare kujerar gwamnan jihar Kaduna da ya wuce ɗan siyasan da mutane suka sani sannan suka shaideshi kan abubuwan Alkhairi’ da yake yi wa mutane.
1 – Sanata Uba Sani mutum ne mai kishin jihar Kaduna da al’ummar ta. Idan za a yi la’akari da daɗewar sa a siyasar Kaduna da irin goyon bayan da yake bayarwa din n cigaban ta shine ya fi cancanta jam’iyyar APC ta tsayar ɗan takaran ta.
2 – Sanata Uba Sani mutum ne mai kowa nashi, sannan da sanin ya kamata.
3 – Arziki da Ɗaukakan da Allah yayi masa bai rufe masa ido ba. A duk lokacin da ka bukaci ganin sa za ka ganshi cikin sauki.
4 – Mutum ne mai tausayin talaka da kuma biyayya da na gaba da shi.
5 – Akwai Sanata Uba Sani da rikon amana. A tsawon kusancin sa da gwamna El-Rufai, a kullum ka yi masa magana game da gwamna El-Rufai, Sanata Uba zai wasa maka shi ne da kuma yaba masa.
6 – Sanata Uba yana kishin matasa. Idan Ka duba zagaye da shi zaka ga duk matasa ne ke amfana da kusancin su da shi a koda yaushe.
7 – Rikon ga addini da tallafa wa addini iya gwargwadon sa. Sanata Uba ya na kokarin tallafa wa addini matuka kama daga masallatai da kuma makarantun islama a fadin jihar Kaduna.
8 – Sanata Uba na da zumunci da alkawari.
9 – Yana da jin shawara da hakuri a ko da yaushe.
10 – Tawakkali da haɗin kai sannan kuma da tausayi.
Waɗannan Kaɗanne daga cikin halayen sanata Uba Sani, wanda nake fanin babban abin da ƴaƴan jam’iyyar APC za su yi su saka wa sanatan shine dungurungum ɗin su su mara masa baya ya zamo ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar APC.