Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Magoya bayan Buhari na jihar Jigawa Musa Gambo-Guri ya bayyana cewa dakatar da limamin masallaci Apo sheikh Nuru Khalid wanda kwamitin masallacin Juma’a na APO ƙarƙashin shugaban kwamitin Sanata Saidu Ɗansadau bai dace ba kuma babu bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari a ciki.
Idan ba a manta ba a cikin karshen makon jiya ne aka dakatar da sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin juma’a na Apo don ya bayyana wasu daga cikin ra’ayoyin sa game da kisan kiyashi da ke yi wa ƴan Najeriya a sassan ƙasar nan.
Sheikh Khalid ya yi kira ga gwamnatin shugaba Buhari da ta samar wa mutanen Najeriya da tsaro kamar yadda ta yi alkawari shekaru kusan 7 da suka gabata.
” Lalacewar ya kai lalacewa, domin yanzu ana kashe mutane a Najeriya kamar kaji ne kuma shugaba Buhari bai yin komai akai, a kullum abin sai ƙara taɓarɓarewa ya ke yi” Inji Khalid.
Sai dai kuma awowi kaɗan bayan kammala sallar juma’a , sai kwamitin masallaci ƙarƙashin Ɗansadau suka sanar da dakatar da malamin wai don jawo hankalin shugaban kasa da yayi game da halin da tsaro ke ciki.
A martanin da ya maida wa Ɗansadau, sheikh Khalid ya ce ba zai janye daga faɗin gaskiya da kira ga shugaba Buhari ya tsawata wajen kawo karshen kashekashe da a ke yi a kasar nan ba ko da ko zai hakura da limanci ne ya koma yin dako a kasuwa.
Musa Gambo-Guri ya ce a matsayinsa na magoya bayan shugaba Buhari suna maraba da irin waɗannan kalamai na tunatarwa da ake yi wa shugabanni, kuma Buhari ba shi da masaniya game da dakatar da sheikh Khalid.
” Ina son mutane su fahimta cewa abinda Sheikh Nuru Khalid yayi ba wani abu ne sabo ba. Gaskiyace ya faɗi kuma muna goyon bayan sa. Malamai kamar su Sheikh Bala Lau ya faɗi wa Buhari a gaban sa cewa mutane na buƙatar gwamnati ta taimaka musu da abinci saboda watan azumi da aka tunkara.
Haka kuma shima sheikh Bello Yabo wanda abubuwan da suke faɗi ya nunka abubuwan da sheikh Nuru Khalid ya fadi.
” Abinda aka yi wa Sheikh Nuru Khalid, ba Buhari ne ya sa aka yi ba, Buhari bai san an yi ba, Ɗansadau ya yi gaban kan sa ne kawai . Ko dai yayi don a bashi wani abu ne ko kuma wasu suka biya shi ya yi haka don ya bata Buhari.