Tsohuwar shugabar Hukumar Kula da Tashoshin jiragen Ruwan Najeriya, NPA kyma shugabar kungiyar ‘#BringBackOurGirl’ Hadiza Bala Usman ta bayyan cewa ko bayan da ta ɗarewa kujerar shugabancin hukumar NPA ta cigaba gwagwarmayar a ceto ƴan matan Chibok da sauran mutane da aka Yi garkuwa da su a kasan.
Hadiza ta fadi haka ne bayan rahotanni sun nuna cewa gwamnati ta kori Hadiza daga aiki a dalilin rubutun da ta yi a shafinta na tweeter kan ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a kasar nan musamman ‘yan matan Chibok da suka yi shekara takwas a hannun mahara.
Hadiza ta ce a shafinta na tweeter @hadizabalausman za a ga yadda ta ci gaba da neman a ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a kasar nan domin a shafinta ta yi magana akan ceto ‘yan matan Chibok, Yara maza na Kangara da sauran matsalolin rashin tsaro da ake fama da su a kasar shekaru hudu da suka gabata.
Kafin gwamnati ta dakatar da Hadiza daga aiki a Mayun 2021 ‘ya Najeriya sun dauki rubutun da ta yi a shafinta na tweeter a watan Febrairun 2021 inda ta yi maganan cewa rashin tsaron kasar nan ya sa aka yi garkuwa da dalibai mata a Zamfara da maza a Kagara da yin kira ga gwamnati ta maida hankali wajen ceto su
‘Yan Najeriya na zargin cewa wannan rubutun da ta Yi ne ya sa gwamnati ta cire ta da daga shugabancin hukumar NPA.
Duk wanda ya ce wai sai yanzu ne na ke wage baki ina cigaba da kira ga gwamnati a ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, bai yi min adalci ba. Domin ko a lokacin da nake gwamnati, ban boye rayina ba game da waɗanda aka yi garkuwa da su.
” Na gana da shugaban kasa sau da dama ina sanye da bajin a ceto ƴan matan Chibok, koma na sha fadin matsaya ta akai. Hatta hoto na da aka makala a NPA da bajin a jikin sa.
Hadiza ta ce wannan abu da aka bijiro da shi wani makirci ne da makiya na ke kitsawa kamar yadda suka saba don suga baya na.
Discussion about this post