Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sau huɗu ya na tsayawa takarar zaɓen gwamna, amma bai yi nasara ba, sai a karon ƙarshe a zaɓen 1999.
Atiku ya bayyana haka a ranar Talata, lokacin da ya ke ganawa da shugabannin ƙungiyoyi sama da 200 a Abuja.
Atiku ya ce a yanzu ya na farin ciki sosai ganin yadda matasa suka zabura wajen kutsawa ana damawa da su a fagen siyasa.
Ya ce muradin sa shi ne idan har ya yi nasara, to ya ga shi kuma ya damƙa mulki a hannu masu jini a jika sosai.
“Abin ya na yi min daɗi ganin yadda a yanzu matasa ke zo min da shawarar neman tsayawa takara a Majalisar Tarayya, akwai masu neman fitowa takarar gwamna ma.
“Hakan ya nuna dimokraɗiyya na ƙara samun inganci kenan.
“Ni ma tun ina kamar ku na fara gwagwarmayar siyasa. Na fara tun ban kai shekaru 40 ba. Amma mu a lokacin ƙoƙarin mu shi ne ganin mun kori sojoji daga kan mulki, mu dawo da dimokraɗiyya.
“To amma fa siyasa sai kun nuna mata juriya, ƙwazo da kuma haƙuri. Misali ni kai na sai da na tsaya takarar gwamna sau huɗu, amma sai a na huɗun sannan na yi nasara a zaɓen 1999.”
Ya gode wa shugabannin ƙungiyoyin dangane da irin goyon bayan da su ka ba shi a zaɓen 2019. Sannan ya ce ya ƙara farin cikin ganin tsarin da su ka fitar a yanzu, wanda ya ce ya ma fi na 2019 ɗin.
“Tsarin mu na yanzu ya ma fi na 2019. To sai mu ɗauki darasi daga 2019. Darasin da muka koya a 2019 ya kasance mana idon mu ya ƙara buɗewa sosai. Dama daga darasi ake samun ƙarin ilmi.
“Abin da na ke nufi a shi ne, an samu kura-kurai a baya. To a yanzu mu na da damar da za mu gyara kura-kuran.”
Shugaban Gambizar Kungiyoyin Kamfen ɗin Atiku, wato Raymond Dokpesi, ya ƙalubalanci shugabannin ƙungiyar cewa su yi rangadin faɗin ƙasar nan, domin su gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP.