Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Babban Limamin Ɗariƙar Katoliƙa, Mathew Hassan-Kuka da nuna tsananin ƙiyayyaga Gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma amfani da mimbarin addini ya na yaɗa farfagandar siyasa domin cimma ɓoyayyar manufar sa.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka a matsayin raddi ga wasu kalaman da Kukah ya yi a saƙon sa na Easter, inda ya zargi Gwamnatin Buhari cewa ta gaza ko ta wane fanni.
“Hassan Kukah ya yi amfani da mimbarin yin huɗuba a coci, maimakon ya tunatar da mabiya Kirista labarin ‘wafati’ da dawowar Annabi Isa (AS), sai ya ɓuge ya na ragargazar gwamnati ta hanyar da bai dace a ce babban mutum kamar sa ya yi ba. Kuma haryar da ba ta kamata ba Kirista na ƙwarai ya yi ba.”
“Bishop Kukah ya yi amfani da lokacin huɗubar sa ya kama faɗan babu gaira babu dalili kan dokar da bai sani ba. Irin yadda ya lissafo matsalolin wannan gwamnati ya nuna irin zurfin yadda Kukah ya tsani wannan gwamnatin baki ɗaya.” Inji Garba Shehu.
PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda Hassan Kukah ya yi yi huɗubar saƙon sa na lokacin Eater, inda a ciki ya ce Buhari ya lalata Najeriya baki ɗaya.
Kukah ya zargi Buhari da cewa ya na sane ya bari cin hanci da rashawa su ka samu gindin zama a cikin gwamnatin Buhari.
Sai dai kuma cikin martanin da Garba Shehu ya yi masa, Fadar Shugaban Ƙasa ya ce maganganun Kukah tsantsar ƙiyayya ce kawai, domin ya kasa kawo hujjojin zargin da ya ke yi.
“Ba mu yi mamaki ba da Bishop Hassan Kukah ya samu lokaci a yanzu ya riƙa huce-haushin sa ga wanda ya saba, Shugaba Muhammadu Buhari.
“Mutumin da ya yi ƙaurin-suna shekara da shekaru ya na watsa bayanan ƙiyayya da nifaƙa, ai babu wani sabon abu kuma da zai sake faɗi, wanda a baya bai taɓa faɗi ba. Sai dai kawai a wannan lokacin, amfani ya rimbarin huɗubar sa a Coci ya na furta kalaman da ba su dace da mutum kamar sa ba.”
Shehu ya ce ƙiyayya da nifaƙa sun rufe wa Kukah ido har ya manta da cewa a kan mimbarin addini ya ke, ba kan duro ɗin kamfen ɗin siyasa ba.
Garba Shehu ya ƙara da cewa Kukah ya yi watsi da koyarwa da horon da aka yi wa Kiristoci a cikin Linjila, Sura ta 1, Aya ta 26:
“Idan ɗaya daga cikin ku ya na jin cewa shi ya fi saura imani, amma bai yi wa harshen sa linzami ba, sai ya riƙa yaudarar zuciyar sa, to ibadar da wannan mutum ya ke yi ba ta da wani amfani gare shi.”