Shugaba Muhammadu Buhari ya yafe wa tsohon Kwamandan Soja, Enitan Ransome-Kuti, Kwamandan Sojojin Haɗin-guiwar MJTF, wanda aka ɗaure saboda laifin dafe ƙeya ya tsere, ya kasa tunkarar Boko Haram.
An ɗaure shi cikin watan Janairu 2015, zamanin mulkin Goodluck Jonathan.
Enitan ɗa ne ga gogaggen ɗan taratsin nan marigayi Beko Ransome-Kuti, kuma ɗan’uwa ga Fela Ransome-Kuti.
An yafe masa shi da wasu mutum 162, ciki har da tsoffi gwamnoni biyu, Joshua Dariye na Filato da Jolly Nyame na Taraba, waɗanda aka ɗaure kotu ta kama su dumu-dumu da laifin satar biliyoyin kuɗaɗen da za a yi wa talakawan jihohin su ayyukan inganta rayuwa.
Kotun Musamman ta Sojoji ce ta kama Enitan da laifi kasa zuwa ya tunkari Boko Haram, a lokacin ya na Kwamandan MJTF a Baga, Jihar Barno.
A lokacin dai Enitan ya tsere, amma aka kamo shi, aka tsare, sannan aka yanke masa hukuncin ɗaurin wata shida kuma aka rage masa igiya daga Burgediya-Janar zuwa Kanar. Bayan nan kuma aka kore shi daga aikin soja.
PREMIUM TIMES ta gano cewa an janye hukuncin na sa ne bisa dalili na tausayi.
Fitaccen mai kare haƙƙin jama’a Femi Falana ne lauyan Enitan da wasu sojoji 60. Kuma shi ya rubuta wasiƙar neman a jingine hukuncin da aka yi masu.
Daga nan ne Majalisar Sojojin Najeriya ta soke ɗaurin watanni shida na Enitan Ransome-Kuti, sauran sauran sojoji 60 da aka yanke wa hukuncin kisa kuwa, aka rage zuwa ɗaurin shekaru 10, sanadiyyar wasiƙar da Femi Falana ya rubuta.
Daga nan kuma ya rubuta wasiƙa ga hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Kwamitin Shugaban Ƙasa, ya nemi ya ma yafe masu baki ɗaya.
Falana ya rubuta wasiƙar neman a soke hukuncin, kuma a yi masu afuwa, saboda su na da dalili ko hujjar guduwa daga yaƙi da Boko Haram.
Hujjar da Femi Falana ya kafa ita ce, sun gudu ne saboda an kasa samar masu da ingantattun makaman da za su iya tunkarar Boko Haram da su.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Buhari ya yafe wa Dariye, Nyame laifin satar kuɗin talakawa, ya yi wa wasu 157 afuwa.
Majalisar Ƙolin Najeriya ƙarƙashin ikon Shugaba Muhammadu Buhari ta yafe wa tsohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye da tsohon Gwamnan Taraba, Jolly Nyame, waɗanda yanzu haka ke ɗaure a kurkuku, bayan yanke musu hukuncin satar maƙudan kuɗaɗen talakawan jihohin su.
Gwamnonin biyu a cikin mutum 159 da aka yafe wa laifukan da su ka aikata, a taron da Majalisar Ƙoli ta yi ranar Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa.
Daga cikin sauran waɗanda aka yafe wa ɗin, akwai tsohon janar kuma Minista a zamanin mulkin Abacha, Tajudeen Olariwaju, Kanar Akiyode, tsohon hadinin Mataimakin Abacha, watau Janar Oladipo diya da sauran dukkan jami’an sojojin da aka ɗaure waɗanda aka kama da laifin yunƙurin juyin mulkin Gideon Orkar, cikin 1990.
Majiya daga Fadar Shugaban Ƙasa ta ce an yafe wa Dariye da Nyame ne bisa dalillai na rashin lafiya da kuma tsufa.
Shekarun Nyame 66, ya yi Gwamnan Jihar Taraba daga 1999 zuwa 2007. An ɗaure shi shekaru 12 a kurkukun Kuje. A cikin 2020 ne Kotun Koli ta jaddada amincewa da ɗaure shi.
Shi kuma Dariye shekarun sa 64. Ya yi Gwamnan Filato daga 1999 zuwa 2007, ya na kurkuku ne saboda satar Naira biliyan 2. An ɗaure shi ya na sanata cikin 2018. Amma bai tafi kurkuku ba har sai da ya kammala wa’adin sa cikin 2019.
Da farko kotu ta ɗaure shi shekaru 14, amma Kotun Ƙoli ta maida hukuncin shekaru 10.
Taron Majalisar Ƙoli dai ya samu halartar dukkan tsoffin shugabannin Najeriya da ke raye, in bada Olusegun Obasanjo, wanda a yanzu haka ke Amurka ana duba lafiyar su.
Su Wane Mambobin Majalisar Ƙoli:
1. Shugaban Ƙasa (shugaban majalisa).
2. Mataimakin Shugaban Ƙasa (mataimakin shugaban majalisa).
3. Dukkan tsoffin shugabannin Najeriya na dimokraɗiyya da na soja.
4. Dukkan tsoffin Shugabannin Kotunan Najeriya.
5. Shugaban Majalisar Dattawa.
6. Kakakin Majalisar Tarayya.
7. Dukkan gwamnoni masu mulki a yanzu.
8. Antoni Janar na Tarayya, Ministan Shari’a na yanzu.