A wannan lokaci da siyasa ta kunno kai a ƙasar nan, shugaban kasa da jigajigan ƴan siyasan Najeriya suna ta wasa wuƙaƙen su domin tunkarar gagarimin abin da ke tafe.
A dalilin haka a bana sai buɗa baki ya zama wani salon haɗa mutane a siyasance.
A cikin makon jiya,uwargidan shugabam kasa A’isha Buhari ta gayyaci ƴan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da wasu gaggan ƴan siyasa domin su zo su yi buɗe baki da ita a fadar shugaban kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari shima ya aika da irin wannan gayyata ga wasu zaɓabbun ƴan siyasa su garzayo fadar Aso Rock su yi buɗe baki da shugaban kasa.
Waɗanda aka gayyata sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC sannan kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, sannan akwai Bisi Akande, sai kuma John Oyegun, Adams Oshiomhole,Ali Modu Sheriff, Bukar Ibrahim, Sani Yerima, Aliyu Wamakko, Oserheimen Osunbor, Olusegun Osoba, da Martala Nyako.
Sauran sun hada da Abubakar Girei, Nasiru Dani, Fati Bala, Tijjanni Tumsah, Abba Aji, Lawal Shuaib da Mohammed Magoro.
Tinubu ne ɗan takarar shugaban kasa ɗaya tilo cikin duka ƴan takarar da ke neman shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar APC da Buhari ya gayyata a wannan buɗe bakin.