A ranar Laraba ne ‘yan bindiga wanda ake zargin Boko Haram ne suka kashe mutum 12 a garin Geidam dake jihar Yobe.
Mazaunan garin sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun afka wa wani gidan giya ne da misalin karfe 10 na dare a daidai ana maskewa.
Sun Kuma ce maharan sun babbake gidajen da malaman makarantar kimiya da fasaha GSTC.
PREMIUM TIMES ta ji daga majiya cewa wasu mutane sun ji rauni a dalilin harin kuma suna babban asibitin Geidam ana duba su.
Wani jami’in tsaro da baya so a fadi sunan sa saboda ba a bashi izinin magana da manema labarai ba ya ce maharan sun zo bayan gari da baburan su amma sai suka ajiye baburan suka karisa cikin garin a kafa.
“Maharan sun Kona gidajen malamai uku. Daga nan mun Kuma samu labarin cewa maharan sun afka gidan karuwai dake Augwar Kweri inda suka kashe mutane 11.
Wani mazaunin garin Idris Abubakar ya ce mutum daya ya mutu a GSTC Geidam.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnan jihar Mai Mala Buni ya dage dokar hana amfani da babura a wasu sassan jihar.
Gwamnati ta hana amfani da babura a jihar saboda yadda mahara ke amfani da su wajen kai wa mutane harehare.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Dungus Abdulkareem ya tabbatar da harin yana mai cewa cikin mutanen da maharan suka kashe akwai tsohon dan sanda da ya yi ritaya sannan da mata biyu.
Discussion about this post