Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana dalilan da su ka sa Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun amincewa da yi wa tsoffin gwamnonin Filato da Taraba afuwa.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Buhari, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya ce Buhari ya yi masu afuwa ne saboda dalili na rashin lafiya da ke damun tsoffin gwamnonin biyu, Joshua Dariye da Jolly Nyame.
Yayin da Dariye ke fuskantar ɗaurin shekaru 10, shi kuwa Nyame zai shafe shekaru 12 ne a kurkuku.
An yi masu afuwa ne tare da wasu mutum 155, ciki har da waɗanda su ka yi wa tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida yunƙurin juyin mulki, cikin 1990.
Garba Shehu ya ce afuwar da aka yi wa su Dariye ba ta da nasaba da siyasa ko kaɗan.
“Da Buhari bai duba cancantar yi masu afuwa ba, bisa dalilin rashin lafiyar ta su, da an riƙa ce masa ba shi da tausayi, ko a riƙa kiran sa maƙetaci.
Sanarwar ta tunatar cewa dokar Najeriya Sashe na 175 (1) a Kundin Dokokin @1990 ta bai wa Shugaban Ƙasa ikon: “Ikon yi wa kowane irin mai laifi afuwa. Kuma kafin a yi afuwar nan, sai da kwamitin ya zauna ya yi nazarin laifin da su ka aikata tukunna.
Ita wannan doka dai ta ce duk girman laifi, Shugaban Ƙasa zai iya yin afuwa a matakai uku.
Ko dai a sallami mutum baki daya. Ko kuma idan yanke hukuncin kisa ne, shugaba na iya maida shi na ɗauri. Ko a rage wa ɗaurarru shekaru, ko kuma a sallame su baki ɗaya.