Bayan kammala yi wa gawar marigayi Alaafin na Oyo Oba Lamidi Adeyemi sallar jana’iza sai kuma ƴan Sango, al’asar Yarabawa suka suntumi gawar zuwa cikin ɗaki domin a cigaba da yi mata abubuwan da ake yi na al’ada idan sarki ta rasu
Idan ba a manta ba Oba Lamidi ya rasu da safiyar Asabar a asibiti dake Ado Ekiti.
An yi masa Sallah kamar yadda addinin musulunci ya shar’anta amma kuma a matsayin sa na babban basarake a jihar Oyo, daya daga cikin manyan masarautun ƙabilar Yarabawa akwai wasu al’adu wanda ake yi wa gawar kafin a bizine.
An fa ƴan al’adan sun ajiye gawar sarkin a wani ɗaki suna ta yin kirari suna kalamai.
Discussion about this post