Kwamishinan ƴan sandan Kaduna Yekini Ayoku ya bayyana cewa yanzu hanyan Abuja-Kaduna ta samu lafiya kwarai da gaskiya matafiya su bita babu fargabar komai.
Hakan na kunshe ne a wata takarda wanda kakakin rundunar na jihar Kaduna Mohammed Jalige ya saka wa hannu ranar Litinin.
Kwamishina Ayoku ya ce yanzu fa hanya ta yi kyau. Matafiya su kwantar da hankulan su yanzu fa hanya ta yi kyau.
Babban hanyar Abuja-Kaduna ta zama bita da Alwalarka saboda hareharen ƴan bindiga da ya tsananta.
An yi garkuwa da mutane da dama a wannan hanya a tsawon shekaru biyu zuwa uku da suka wuce.
Mutane sun koma shiga jirgin kasa saboda tsaro amma kuma tun bayan kari da ƴan bindiga suka kai dole aka koma bin hanyar mota.
A karshe Jalige ya yi kira ga mutane cewa rundunar ƴan sanda na horon mutane su rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri domin taimakawa wajen gano batagari a cikin al’umma.