Bankin Duniya ya shawarci Najeriya ta cire tallafin fetur kuma ta sake tsarin canji da musayar kuɗaɗen ƙasashen waje
Shugaban Bankin Duniya David Malpass ne ya yi wannan shawarar a ranar Laraba, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, bayan tashi daga taro a Washington DC.
Malpass ya ce zunzurutun kuɗaɗen da Najeriya ke kashewa da sunan biya ko cike gurbin tallafin fetur, za a iya amfani da su a bunƙasa tare da gaggauta ci gaban ƙasar nan.
Malpass ya ce yi wa fetur biyan kuɗin tallafin mai abu ne mai haifar da mummunar illa ga tattalin arzking ƙasa.
“Saboda tallafi abu ne mai jan kuɗi da yawa, kuma ba a san nan da wane lokaci ne wa’adin ranar daina biyan ba.
Ya ce shi tallafin fetur wasu ƙalilan ɗin mutane ne masu hannu da shuni ke amfana da shi.
“Amma kyan tallafi na mai ko na abinci ya kasance jama’a marasa ƙarfi ne ke cin moriyar sa, ba masu ƙumbar susa ba. Dalili kenan mu ke ƙara jaddada wa Najeriya cewa ta canja tunani game da tallafin man fetur.” Inji Malpass.
Cikin makon da ya gabata ne Majalisar Dattawa ta amince da roƙon da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a cikin kasafin 2022 a biya Naira tiriliyan 4 matsayin kuɗaɗen tallafin mai.
Cikin makon da ya gabata ne kuma Ƙaramin Ministan Ferur, Timipre Sylva ya ce wasu tantagaryar gadangarƙama ne ke cin moriyar tallafin mai.
Sylva ya ce tallafin mai na ƙara haifar da sumogal ɗin fetur, lamarin da ya ce ke kawo naƙasu ga tattalin arziki.
Haka nan kuma Bankin Duniya ya gargaɗi Najeriya ta yi fatali da tsarin musayar kuɗaɗe mai harshen-damo, wanda ya ce ya na dagula al’amurran cinikayya da kasuwanci da kuma hana zuba jari a kasar
Discussion about this post