Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ki amincewa da yin murabus ɗin da wasu kwamishinoninsa suka yi ciki harda shugaban fadar gwamnatin sa.
Sai dai kuma akwai wasu kwamishinonin 6 da Ganduje ya amince da ajiye aikin su domin shiga yin takara da siyasa.
Cikin waɗanda aka amince da murabus ɗin su sun haɗa da kwamishina ƙananan hukumomi, Sule Garo wanda ya bayyana aniyarsa na yin takarar gwamna a jihar Kano.
Sauran kwamishinonin sun haɗa da na Al’adu, Ibrahim Ƙaraye da na gidaje Mahmud Muhammed. Sai kuma Muntari Yakasai, Musa Kwankwaso da Kabiru Lakwaya.
Waɗanda kuma gwamna Ganduje ya ki amincewa da
murabus ɗin su sun hada da Sanusi Ƙiru na Ma’aikatar Ilimi, Ibrahim Aminu na Kiwon Lafiya da Nura Ɗankadai na kasafin kuɗi.