Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya bayyana cewa Najeriya a matsayin ta na ƙasa, ba ta da sauran dukiyar da za a riƙa yin watanda da ita idan an hau mulki, kamar yadda aka riƙa yi daga shekaru 40 baya.
Ya ce duk mai son zama shugaban ƙasa, to ya yi shirin tara wa ‘yan Najeriya dukiyar da zai yi masu watandar tukunna.
Obaseki ya yi wannan furucin a Benin babban birnin Jihar Edo, lokacin da ya karɓi baƙuncin ‘yan takarar shugaban ƙasa su huɗu a ƙarƙashin jam’iyyar APC da su ka kai masa ziyara.
“Shekaru arba’in da su ka gabata mu na da gabjejen akushi cike da tuwon da ake watanda. Amma ya a yau babu akushin kuma babu tuwon da za a yi watandar.
“Duk mai son zama shugaban ƙasa tilas ya zama mutumin da ‘yan Najeriya suka amince za su ba shi damar samar wa ƙasar nan ƙasaitaccen tattalin arziki baki ɗaya.
“Kamar mu yanzu a Jihar Edo, mun shirya zama dakalin gina babba, ƙasaitacciya kuma attajirar Najeriya. Saboda ba za mu iya ci gaba da kasancewa a yadda mu ke tafiya a yanzu ba.
“Mun damu sosai cewa sai fa PDP ta dawo ta jawo ‘yan Najeriya a jika sannan za ta iya fita daga ƙuncin da ƙasar ke fama shi.
“Abubuwa sun taɓarɓare, mutanen mu na cikin wani mawuyacin hali. Ba mu taba jin jiki kamar yadda mu ke fama a yanzu ba.
“Ba mu taɓa fama da tantagaryar fatara da yunwa da kuma tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci da masarufi irin yadda ake ta fama ba kamar yanzu. Fatara da da tsadar rayuwa sun danne miliyoyin jama’a, sun kwantar da wasu masu yawan gaske. Ga kuma gagarimar matsalar tsaron da ake fama da ita a faɗin ƙasar nan.
“An yi garkuwa da ɗimbin mutane a cikin Najeriya. A yanzu ɗin nan da na ke magana ɗimbin mutane na hannun masu garkuwa da mutane.”
Obaseki ya gode masu, kuma ya nuna cewa masu neman takarar na da basirar kai Najeriya gacin da ake ta mafarkin ta kai. Ya ce haka ake so a ga masu fama da ƙoƙarin kawo shugabanci nagari sun haɗe kan su domin ciyar da al’umma gaba.
“Su na ƙoƙarin ganin sun fito da ɗan takara ɗaya tsakanin su, ta hanyar cimma yarjejeniyar janyewar sauran abokan takara.
Tun da farko dai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya yi bayani a madadin sauran da su ka haɗa da Mohammed Hayatuddeen, Bala Mohammed da Aminu Tambuwal.
Ya ce sun je Benin ne domin gabatar da shawarar cewa PDP ta zaɓi ɗan takarar ɗaya wanda sauran za su janye masa ya tsaya wa PDP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
“Ba so mu ke yi duk mu ƙarar da ƙarfin mu ko kuzarin mu wajen neman mulki. Buƙatar mu kawai ita ce mu gina ƙasaitacciyar Najeriya.” Inji Saraki.
Discussion about this post