Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, kuma gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike ya bayyana cewa a irin ƙaunar da yake yi wa PDP baya ganin ko ya faɗi zaɓen fidda ɗan takara zai koma wata Jam’iyyar.
Wike ya ce” ko na yi nasara a zaɓen fidda gwani, ko ban yi ba, PDP zan cigaba da yi babu gudu ba ja da baya.
Idan ba a manta ba gwamnan Ribas, Nyesome Wike ya fito takarar kujerar shugaban kasa a a zaɓen 2023.
Sai dai kuma akwai jan aiki a gaban sa domin, akwai ƴan takara da dama da gaban sa wanda suma kujerar ce a gaban su.
Cikin su akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Aminu Tambuwal da Anyim Pius Anyim da dai sauran su.
Wike ya kai ziyarar ganawa da wakilan jam’iyyar a garin Minna Jihar Neja.
Wike ya ce ” Idan kuka zaɓeni ɗan takaran ku, ku sani baku yi asara ba, domin kasar nan na bukatar mutum jarimi, gogagge sannan mara tsoro.
” Najeriya na bukatar mutumin da idan yaga abu fari zai ce wannan abu fari ne, babu tsoro ko fargabar wani abu zai faru.
” Wannan mutum kuma ni ne, saboda haka ina neman kuri’un ku a zaɓen fidda gwani da za a yi domin mu kai ga nasara.