Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa kashi 42% bisa kashi 100% na sabbin rajistar katin zaɓe duk haramtattu ne, domin ba a cika su bisa ƙa’ida ba.
Shugaban INEC Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke gabatar wa manema labarai da samfurin Sabbin Katin Rajistar Zaɓe, a hedikwatar hukumar a Abuja.
Yakubu ya ce a yanzu akwai sabbin Katin Rajistar Zaɓe na Dindindin (PVC) guda 1,854,859 waɗanda INEC za ta raba wa masu su a faɗin jihohin ƙasar nan 36 da Abuja.
Shugaban na INEC ya ce za a raba katin da zaran an koma aiki, bayan hutun ‘Easter’.
Tun dai da aka fara sabuwar Rajistar Katin Zaɓe a ranar 28 Ga Yuni, 2021, miliyoyin ‘yan Najeriya su ka bazama wajen yin rajista domin samun damar dangwala ƙuri’a a zaɓen 2023.
Daga cikin adadin waɗanda su ka yi rajista tsakanin Yuni da Disamba, 2021, kashi 55 cikin 100 aka tabbatar da sahihancin su.
Hakan ya na nufin kenan kashi 42 cikin 100 na rajistar da aka yi duk ta zama a banza, ba su inganta ba, wasu INEC ba za ta bari a yi zaɓen 2023 da su ba.
Yakubu ya bayyana cewa yin rajista fiye da sau ɗaya da kuma rashin cike gurabun fam ɗin daidai ne suka haddasa matsalar.
Shugaban na INEC ya ce ƙarin abin takaicin kuma shi ne yadda aka samu wasu ma’aikatan INEC da hannu dumu-dumu wajen yi wa wasu rajista sau biyu, lamarin da ya Kububu ya ce “abin damuwa ne matuƙa idan aka yi la’akari da lokacin da aka ɓata da kuɗaɗen da aka kashe a wajen tsawon lokacin da aka ɗauka ana aikin sabunta rajista ɗin.
“Saboda haka wannan hukuma na nan ta na binciken duk wani ma’aikatacin da aka samu da hannu a cikin wannan abin takaici, to za a gurfanar da shi kotu.
“Haka wasu da suka yi rajistar su ma za a kamo su su a gurfanar da su koru, domin a hukunta su kamar yadda Sashe na 22 da 23 na Dokar Zaɓe ta 2022 ta tanadar.
Yakubu ya ce INEC ta yi amfani da tsarin tantance sahihiyar rajista da rajistar jabu na ABIS, wanda ke gane fuskar wanda ya yi rajista sau biyu, kuma tsarin gane mutum idan ya yi rajista fiye da ɗaya, wato hanyar dangwala yatsa ta ‘fingerprint.’