Idan mai karatu ya ce su Dogo Giɗe da Ali Kachalla sun gagari gwamnati, to ko maka shi aka yi gaban alƙali, zai iya yin nasara matsawar ya lissafa ko da kaɗan ne daga irin aika-aika ko ɓarnar da su ke yi kan su tsaye a cikin jama’a.
Haba jama’a! Ɗan bindigar da zai kai wa filin jirgin sama da barikin soja hari, ya gagari gwamnati ko bai gagari gwamnati ba? To ya dai gagare ta ɗin.
Ɗan bindigar da zai yi fashin jirgin ƙasa, ya kwashe fasinjoji don kawai ya tilasta gwamnati ta saurare shi, kuma ta biya masa buƙatar sa, shin ya gagari gwamnati ko bai gagare ta ba ma, ya gagare ta ɗin.
Haba jama’a! Ɗan bindigar da zai kwashe ɗalibai maza da mata, daga baya ya sako maza ya zaɓi wasu matan da yawa ya aurar da su ga kwamandojin sa, zancen gaskiya ya gagari gwamnati.
Inda ma abin ya fi ciwo, shi ne yadda ‘yan bindigar ke rako ‘amaren na su’ har cikin garin su na haihuwa, a yi masu ƙunshi da lalle. Idan an gama kuma a sake tasa ƙeyar su zuwa cikin daji. Babu wanda ya isa ya ɗaga yatsa. Sun fi ƙarfin gwamnati ko ba su fi ƙarfin gwamnati ba, ya rage wa mai karatu ya faɗa wa kan sa gaskiya.
Ɗan bindigar da ke ƙwace garuruwa har ya kafa masa irin dokokin da ke so su riƙa yin rayuwar su, ko ba ka kira shi ‘gwamnati’ ba, ai ka kira shi ‘ka-fi-gwamnati.’
Daula Da Duniyar Dogo Giɗe: Ɗan Bindigar Da Ya Haramta Karuwai, Giya Da Muggan Ƙwayoyi A Daular Sa:
Dogo Giɗe na ɗaya daga cikin riƙaƙƙun ‘yan ta’addar da suka yi haɗin-gwiwar kai wa jirgin ƙasa hari a dajin Kaduna, ranar 28 Ga Maris, 2022.
A yanzu dai za a iya cewa Giɗe ya fi duk wani gungu, daba ko garken ‘yan bindiga karɓar kuɗin fansa a Arewa ko ma a Najeriya arankatakaf.
Shi Dogo Giɗe, akasari ya fi kai farmakin sa a ma’aikatu, hukumomin gwamnati da kuma kan jami’an gwamnati.
Ya fi maida hankali wajen yi wa gine-ginen gwamnati dirar mikiya, irin su makarantu da kuma matafiya saboda wasu dalilai.
‘Shari’ar Musulunci’ A Daular Dogo Giɗe:
Ba kamar sauran gungu-gungun ‘yan bindiga inda ake fyaɗe, jigilar karuwai da shaye-shayen ƙwayoyin ko tambayewa cikin ayyukan masha’a ba, shi Dogo Giɗe ya haramta waɗannan kaba’irori da Dajin Kuyanbana, inda ya kafa sansanin sa a cikin Jihar Zamfara.
Giɗe ya yi ƙarfin da ya yi wa sauran ‘yan bindiga gargaɗi da kashedi ga sauran ‘yan bindigar da ke maƙautaka da sansanin sa cewa su daina kai gare a ƙauyukan da ke kusa da shi, ko kuma su yaba wa aya zaƙi.
Wasu majiyoyi sun shaida wa wakilin mu cewa an ɗan samu sauƙin kai hare-hare a wasu yankunan cikin Zamfara saboda gargaɗin da Giɗe ya yi wa ‘yan bindigar.
Dogo Giɗe, shi da gwamanti ya ke faɗa ba da mutanen gari ba. Ya sha alwashin sai ya tatsi gwamnati, kuma sai ta yi masa kuka da hawayen ta.
Da alamu an kamo hanyar yin haka, bisa la’akari da bayan raɗa wa ‘yan bindiga sunan ‘yan ta’adda cikin Nuwamba, 2021, maimakon abin ya yi sauƙi su razana su ɓoye, sai ma su ka ƙara fitowa fili gabagaɗi, har suka kai wa jirgin ƙasa mummunan hari cikin watan Maris, 2022.
Kafin nan har ma sai da suka kai farmaki Cibiyar Horas Da Hafsoshin Sojoji ta farko a Najeriya da ke Kaduna, NDA.
Yadda Dogo Giɗe Ya Zama Gagarau A Gaban Gagarabadau:
Dogo Giɗe ya fara shahara ne tun daga ranar da ya kashe Tsoho Buhari cikin 2018. Kafin kashe shi, Buharin Daji ne mafi hatsabibanci n da aka fi tsoro a yankin dazukan Zamfara.
Giɗe yaron Buharin Daji ne kafin ya kashe shi, sanadiyyar Buhari ya kwashe shanun surikin Dogo Giɗe.
Kashe Buharin Daji ya ƙara wa Dogo Giɗe girma a cikin ‘yan bindiga, domin an kasance ana tsoron Buhari, har ana tunanin albarushi ba ya iya keta jikin sa. Kuma, raɗe-raɗin har layar-zana gare shi.
Daga nan ne daular Giɗe ta ƙara faɗaɗa a kusa da nesa sosai.
Abokin Damo Guza: Alaƙar Dogo Giɗe Da Boko Haram:
An haifi Bafulatani Dogo Giɗe a yankin Erana, cikin Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.
Giɗe ya yi makarantar allo a makarantar Isah Erana, tsohon limamin garin Erana.
Ba za a ce ga daga lokacin da ya fara sata da fashi ba, amma dai Dogo Giɗe ya zama ƙasurgumin ɗan fashi lokacin da ya fara kai wa ƙauyuka farmaki ya na satar shanu d sauran dabbobi da kayan gona.
Amma ya ƙara maƙasura ne lokacin da ya haɗu da wasu riƙaƙƙun ‘yan Boko Haram da ke da sansanoni a yankin na Shiroro.
‘Tubar’ Dogo Giɗe Daga Kai Wa Ƙauyuka Hari, Ya Koma Kai Wa Ma’aikatun Gwamanti Farmaki:
Yayin da alaƙa ta ƙullu tsakanin Dogo Giɗe da Boko Haram, sai su ka shawarce shi ya daina kai wa mazauna ƙauyuka hare-hare, ya riƙa kai wa gwamnati kawai, musamman makarantun zamani, waɗanda Boko Haram ke cewa haramtattu ne.
‘Ali Ya Ga Ali’: Yadda Abotar Dogo Giɗe Da Tantagaryar Ɗan Bindiga Ali Kachalla Ta Maida Su Dajin Zamfara:
Haɗuwar Giɗe da tantagaryar ɗan bindiga Ali Kachalla ta sa sun kafa babban sansani a Dajin Kuyanbana da ke cikin Jihar Zamfara.
Wasu jami’an tsaron da su ke da masaniyar Giɗe da Kachalla, sun ce a farkon haɗewar su sun riƙa samun manyan makamai daga hannun Boko Haram. Haka dai suka shaida wa PREMIUM TIMES.
Haka kuma jami’an tsaro a Kaduna sun ce idan ka ga ko ka ji an tare hanya tsakanin Abuja zuwa Kaduna, to yaran ɗaya daga cikin su biyun ne. Ko na Giɗe ko kuma na Kachalla.
Yadda Dogo Giɗe Ya Kafa ‘Gwamnatin Karamar Hukuma’:
Mutane da dama masu masaniyar abin da ke faruwa a yankin da Giɗe ke mulki, sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa ya kafa dokokin hana kai wa garuruwan da ke yankin sa hari a Zamfara.
Ya haramta masu kamo mata, kamo mutane su yi garkuwa da su da kuma karɓar kuɗin fansa. Duk tsiyar da Giɗe ke yi, shi dai gwamnati ce ya ke faɗa da ita kawai.
Kuma Dogo Giɗe ya hana yaran sa karɓar kuɗaɗen haraji a ƙauyuka.
Amma kuma ya ba su iznin cewa za su iya su kai farmaki a makarantun gwamanti da ke can wasu yankunan da ba a cikin Jihar Zamfara ba.
Dogo Giɗe Ya Haramta Karuwanci, Giya, Shan Ƙwaya A Babban Doka:
Babban Doka shi ne ƙauyen da Dogo Giɗe ke zuwa ya na Sallar Juma’a kowane mako. Ya hana karuwanci a garin, ya hana sayarwa ko shan giya da dukkan ƙwayoyi masu bugarwa a garin.
“Wata rana ne a Masallacin garin Dogo Giɗe ya yi wannan sanarwar. Ya ce duk wanda aka kama ya na sayar da ƙwaya, za a bindige shi kawai. Kuma ya faɗi haka ne a gaban wasu baƙin-fuskar ‘yan bindiga waɗanda ake zaton abokan sa ne ‘yan Boko Haram.
Ali Kachalla: Ƙasurgumin Ɗan Bindigar Da Ba Ya So ‘Ya’yan Sa Su Gaje Shi:
Ali Kachalla shi ma ya ƙulla alaƙa da Boko Haram, kamar yadda jami’an tsaro su ka tabbatar.
Ya na da mata uku da ‘ya’ya da dama. Sai dai kuma bai saka ‘ya’yan sa ko ɗaya ba a hare-haren da suke kaiwa.
Hasali ma ya nesanta kan sa daga iyalan sa da iyayen sa, don kada ya ja masu fushin jami’an tsaro a kama su.
Iyayen Ali Kachalla na cikin wani yankin Maru zaune da ran su.
Majiya ta ce Ali Kachalla bai kai shekaru 40 ba. Kuma an haife shi ne a wani yanki na Madada, cikin gundumar Ɗansadau.
Ali Kachalla ya fara tashe bayan da Giɗe ya kashe Buharin Daji. Saboda shi ma ɗin Kachalla yaron Buharin Daji ɗin ne.
Amma dai Kachalla, wanda ake kira Kawaje, ya ce ya ƙara suna ne bayan da ‘yan sansanin sa suka kakkaɓo jirgin yaƙin Najeriya cikin watan Janairu, 2021. Daga nan ya ƙara horas da yaran da zai ƙara ƙarfin kai hare-hare.
Yawancin yaran Kachalla duk yaran Buharin Daji ne. Bayan Giɗe ya kashe Buhari, sai yawan sa suka rasa hannun wa za su kasance. Maimakon su zaɓi Giɗe wanda ya kashe Buharin Daji, sai suka bi Kachalla, wanda shi da Buhari da su ɗin duk ‘yan tsatson Fulani ɗaya ne.
Kachalla na da sansanoni da dama a yankin Kaduna da Birnin Gwari. Da shi da Giɗe da ‘yan Ansaru suka haɗa ƙarfi suka kai wa jirgin ƙasa farmaki a Kaduna ranar 28 Ga Maris.
Da farko Kachalla da shugaban Boko Haram ‘yan Ansaru abokan gaba ne. Daga nan kuma sun shirya har su na tafka ta’asa tare.
Mazauna ƙauyen Babban Doko sun ce matan da su Dogo Giɗe su ka aurar a tsakanin yaran su, a kan kawo su har cikin garin a yi masu ƙunshi, tare da rakiyar ‘yan bindiga ɗauke da zabga-zabgan bindigogi.