Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana ranakun 30 da 31 ga Mayu ranakun da za ta yi zaben fidda wanda zai cira tutar jam’iyyar a zaɓen shugaban kasa da ke tafe a 2023.
Sakataren jam’iyyar, Iyiola Omisore ne ya saka hannu a takardar wanda jam’iyyar ta aika wa hukumar zaɓe.
Idan ba a manta ba hukumar zaɓe ta umarci jam’iyyun kasar nan su tabbata sun yi zaɓen fidda gwani da kuma aika wa da sunayen yan takarar kujerun su a farkon watan Yuni.
APC ta ce za ta gudanar da zaben kujeran gwamna a jihohi da na majalisar jihohi a ranakun 23 da 11 ga Mayu.
Wato na gwamna ranar 23, na ƴan majalisar jiha kuma ranar 11 ga Mayu.
Za a yi zaɓen fidda gwani na kujerun majalisar tarayya da na dattawa ranar 18 ga Mayu.
Jam’iyyar za ta gudanar da babban taron ta a ranar Laraba maizuwa wand shine taro na farko da zata yi a ƙarkashin sabbin zaɓaɓɓin shugabannin ta wanda aka yi a watan Maris.
Idan ba a yi samu jituwa tsakanin ƴan takaran jam’iyyar musamman kujerar shugaban, toh ko za ayi kare jini, biri jini a wajen zaɓen ɗan takarar shugaban kasan.
Babban dalilin haka kuwa shine ganin jigajigan jam’iyyar da dama sun fito takarar kujerar shugaban kasa.
Waɗanda za a fafata a tsakanin su kuwa sun haɗa da Bola Tinubu, Rotimi Amaechi, Rochas Okorocha,David Umahi, Orji Uzor Kalu, Yahaya Bello, da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.