Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya rabawa sarakunan jihar Motocin alfarma kowa ya ci gaba da watayawa, talakawa kuma su sha kallo.
An yi bikin raba waɗannan kinkima-kinkiman motoci ne a garin Gusau inda ya samu halarci masu faɗa aji a jihar.
Waɗannan motoci da aka raba wa sarakunan motocine masu tsadan gaske wanda ko man da za a zuba musu na sai mutum ya ci ya koshi.
Wannan motoci da gwamna Matawalle ya raba ya jawo cecekuce tsakanin masu karatu a shafukan yanar gizo inda wasu ke ganin wannan ba shi bane matsalar da ta ke ciwa mutanen jihar Zamfara tuwo a kwarya ba.
” Tsakani da Allah, maimakon a tallafa wa mutane da tsaro da kauda musu da bakin talauci da suke fama dashi kawai sai a wannan lokaci gwamna ya fito ya na raba irin waɗannan motoci ga sarakuna talakawa kuma ko oho” in ji wani mai sharhi a yanar gizo.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsa n su gama da wannan kyauta da gwamna matawalle tayi wa sarakunan suna masu yi tir da kyautar sannan da yin kira ga gwamnatoci su san abinda ya makata su rika yi wa mutane talakawa ba a kullun a rika kara wa mai ƙarfi ƙarfi ba.