An kashe kwamandojin ISWAP biyu da mutum 32 a bata kashin da aka yi tsakanin ISWAP da Boko Haram a dajin Sambisa dake jihar Borno.
Masanin aiyyukan ‘yan ta’adda dake jihar Zagazola Makama ya sanar da haka.
Makama ya ce maharan sun yi barke da ɓarin wuta a tsakaninsu ne a kayukan Yale dake Damboa da Gargash dake karamar hukumar Bama.
“A kauyen Yale Boko Haram sun kashe wasu kwamandojin ISWAP biyu tare da mabiyan kungiyar hudu a wannan arangama.
Makama ya ce Boko Haram ta yi wa kungiyar ISWAP diran mikiya da dare ranar 19 ga Afrilun 2022 a lokacin da suke hijira zuwa wata sabuwar sansanin da suka kafa.
Ya ce Boko Haram ta yi wa mutum hudu din da suka kama da kwamandojin ISWAP yankar rago sannan sun kona motocin bindigar kungiyar guda uku.
Bayan haka Makama ya ce a ranar 20 ga Afrilu 2022 wani kwamandan Boko Haram Ambu Mairamiri tare da mabiyansa sun kai wa ISWAP hari a kauyen Ngurosoye.
Ya ce ISWAP ta rasa mutum 18 su kuma Boko Haram sun rasa mutum 6 a arangamar da aka yi tsawon awa biyu ana yi batakashi.
Wata majiya a rundunar sojin Najeriya a Maiduguri ta bayyana cewa Mairamiri wanda ya lashi takonin gamawa da ISWAP ya kona motocin bindiga hudu.
Zuwa yanzu Boko Haram na farautar ISWAP cikin dare ne su kuma ISWAP su kai harin ramakon gayya da rana.
ISWAP da iyalan su suna can a tsibirin Mandara ya nda suke zaune.
Sauran wuraren da maharan ke boye sun hada da Gargash, Izza, Bula Bakakai, Gobara da dutsen Ngulde dake karamar hukumar Chibok.