Wata ƴar takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APGA ta bayyana cewa Allah ya yi mata wahayin cewa wai ni ce shugaban kasa a Najeriya bayan shugaba Buhari.
” Wannan ba kuskure bane ko kuma ina kantara muku tamalle, Allah da kansa ya yi min wahayi ya gaya min cewa in zauna cikin shiri ni ce zan dare kujerar shugaban kasa a Najeriya a 2023.
” Wasu manyan jam’iyyun kasar nan sun yi min tayi in zo su bani mukamin mataimakiyar shugaban kasa amma na ki saboda ba shine abinda llah yake sona dashi ba. Shugabancin kasar ce yake so na yi.
Angela Johnson, ta kara da cewa maza sun baiwa mutanen Najeriya kunya matuƙa, karara ya nuna ba za su iya ba.
” Yadda matsalolin tsaro da na tattalin arzikin kasa suka dabaibaye kasar nan ana neman jajirtacce mai hangen nesa ne ya ceto kasar nan daga halin da ta tsinci kanta a ciki.
” Ba za mu sa ido ba mu bari shikenan a yagalgala kasar babu madafa ba. Wannan suna daga suna daga cikin dalilan da ya sa Allah ya yi min wahayin in fito takarar shugaban kasa a Najeriya.
” Ina mai shaida wa shugaban jam’iyyar APGA cewa zai zama shugaban jam’iyya na farko da zai samar da shugaban ƙasa mace ta farko a Najeriya.
Discussion about this post