Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta bayyana cewa zuwa yanzu dai aikin Gadar Kogin Neja mai tsawon kilomita 1.6, ya cinye naira biliyan 157 daga cikin naira biliyan 400 da aikin zai lashe kafin a kammala shi.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, a lokacin da kai ziyarar gani da ido na yadda aikin gadar ke tafiya.
Gadar Kogin Neja dai ita ce ta haɗa Arewa da kudancin ƙasar nan. Ita ce a Turance ake kira 2nd Niger Bridge.
Tun da farko Gwamnantin Tarayya ta bayar da kwangilar kan naira biliyan 206, amma daga baya dai an maida kwangilar naira biliyan 400, bisa dalilai na tsadar kaya da tashin farashin kayan gini.
A yayin ziyarar da Minista Zainab ta kai, Gwamnan Jihar Anambra Charles Soludo ne ya karɓe ta, a ƙarƙashin wakilcin Mataimakin Gwamna Onyeka Ibizim.
A wurin tarbar ministar har da Shugaban Hukumar NSIP Uche Orji da kuma wakilin Kamfanin Julius Berger.
Ma’aikatar Harakokin Kuɗaɗe ce ke bibiyar aikin sa kuma tabbatar da biyan kuɗaɗen a ƙarƙashin shirin PIDF da kuma NSIA.
“Na yi farin ciki da irin ci gaban da aka samu wajen aikin ginin wannan gada. Zan iya zuwa kai tsaye na shaida da Shugaba Muhammadu Buhari cewa na ga inda aka kashe naira biliyan 157. Aiki kuma ya na kyau sosai.”
Zainab ta ce aikin gadar na daya daga cikin muhimman ayyukan da Gwamnatin Buhari ta yi ko ta ke kan yi.
Ta ce idan an kammala gadar, za ta zama silar kawo gagarimin ci gaba da sauƙaƙe hada-hada a yankin na Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma.
Zainab ta ƙara da cewa, “akasarin masu aiki a gasar duk ‘yan yankin ne, kuma kimanin mutum 20,000 ke cin gajiyar aiki a gadar.
“Hukumar PIDF ke biyan kuɗaɗen aikin, a ƙarƙashin NSIA. Kuma aikin titin Lagos zuwa Ibadan da aikin titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Legas duk a ƙarƙashin PIDF/NSIA ake tafiyar da shi.
“Kuɗaɗen da aka ƙwato daga cikin kuɗaɗen da tsohon Shugaban Mulkin Soja, Sani Abacha ya ɓoye a waje, duk su na cikin ayyukan gadar da kuma titinan ne.” Inji Minista Zainab.