Ɗimbin ‘yan Najeriya sun hallara Makka, Saudi Arabiya domin gudanar da Ɗawafi na Musamman, neman nasara kan Bola Tinubu domin yin nasara a zaɓen fidda-gwanin APC da kuma nasarar zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Kakakin Majalisar Jihar Legas Mudashiru Obasa ne ya bayyana haka.
Za a fara Ɗawafin da rana tsaka har zuwa lokacin Sallar Azahar, inda za su riƙa kewaya Ka’aba, su na roƙon Allah Maɗaukaki ya bai wa Tinubu nasarar hawa shugabancin Najeriya, a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Masu yin Ɗawafin za su sanya farin harami, inda kafin su ƙarasa sai sun hallara a ƙofar shiga Ka’aba mai suna Ƙofar Sarki Abdul’aziz.
Ana sa ran wasu manyan malamai da manyan ‘yan siyasa daga Najeriya duk za su halarci ɗawafin, ciki har da Kakakin Majalisar Jihar Legas, Obasa, wanda shi ne ma ya ce kuma za su gode wa Allah (SWT) domin Tinubu ya yi nasara.
Obasa ya ce dukkan waɗanda za su yi ɗawafin dai sun yi imani da Allah cewa Tinubu ne zai yi nasara.
“Mun zo ne domin mu nemi sa’a da biyan buƙatar ganin Tinubu ya yi nasara a zaɓen 2023 ” Inji Obasa.
“Muna neman biyan buƙatar Allah domin Tinubu ya yi nasara.
“Tunda mun san dai mun tuntuɓi dimbin mutane kuma mun yi shirin ganin nasara daga wurin Allah.”
Obasa ya roƙi sauran Musulmi da ke ɗawafin Umra su shiga cikin zugar su, domin a yi ɗawafin tare da su.
Premium Times Hausa ta lura shi ma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa na Saudiyya domin yin Umra.
An nuno hotunan Atiku a gaban Kabarin Annabi SAW ya na addu’a. Kuma an nuno shi a cikin Masallacin na Madina ya na zaune ya na addu’a.
2023: Za Mu Jefa Wa Tinubu Kuri’a Miliyan 14 -Ƙungiyar Sai-Tinubu
Wata ƙungiyar masu goyon bayan ganin Bola Tinubu ya yi nasara a zaɓen 2023, mai suna Tinubu Support Group, ta sha alwashin samo wa Tinubu ƙuri’a miliyan 14 a zaɓen 2023.
Ƙungiyar mai suna South West Agenda for Asiwaju (SWAGA), ta ce su na da kyakkyawar fatan cewa Tinubu na da ɗimbin magoya bayan da za su zabga masa ruwan ƙuri’u a yankin Kudu maso Yamma waɗanda za su iya samar masa aƙalla miliyan 14 na ƙuri’u.
Shugaban Ƙungiyar kuma tsohon Sanata Adedayo Adeyeye ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara ofishin PREMIUM TIMES, a Abuja, a ranar Talata.
Ya ce an kafa SWAGA ce domin tabbatar da burin Bola Tinubu ya cika, na ganin ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023. Kuma ajanda ce ta yankin Arewa maso Yamma.
Ya ce sun kafa ƙungiyar domin zaburar da al’ummar yankin Kudu maso Yamma, domin su zaɓi Tinubu, ganin yadda ba a fito sosai a yankin an jefa ƙuri’a ba a zaɓukan baya.
Ya ce ya tabbatar za a fito a yi ruwan ƙuri’un domin a kawo ƙarshen matsalar tsaro, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Ya ce Tinubu ya samu goyon bayan sarakunan gargajiya na yankin Kudu maso Yamma fiye da 300.
“Magauta da masu mugun baki na cewa Tinubu ba shi da magoya baya sosai a yankin sa na Jihohin Yarabawa.
“Mun ziyarci fiye da Oba 300 kuma duk sun yi masa addu’a tare da sa masa albarka. Jama’a sai harama su ke yi a yankin Kudu maso Yamma su na shiga jirgin lodin ajandar TInubu.
“Ina tabbatar maku idan Buhari ya ce ya na da ƙuri’u miliyan 12, to shi kuma tuni Tinubu na da ƙuri’u miliyan 14 a cikin aljifan mu.” Inji shi.