Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana cewa idan ya zama shugaban kasa a 2023 zai maida ta talakawa akalla miliyan 20 attajirai.
Hakan yana kunshe ne a jawabin da yayi a wajen kaddamar da takarar shugaban kasa ranar Asabar.
Gwamna Yahaya Bello ya ce burin sa shine yaga ƴan Najeriya suna cikin walwala da jin daɗi a ko ina suke.
” A dalilin haka ya sa zama samar da tsare-tsare na koyar da matasa da mutane sana’a da kasuwanci domin su rike kansu. Sannan kuma gwamnati na za ta samar da hanyoyi da zai azurta akalla mutum miliyan 20 su zama attajirai.
Bayan haka gwamna Yahaya Bello ya ce zai duba duk wata hanya da ya dace abi domin kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan. ” Za mu duba korafe-korafen mutane da waɗanda ke ganin ana take su ba a musu ganin su mutane ne mu gyara matsalar kowa ya wataya a matsayin sa na ɗan kasa.
Da yake magana kan jihar sa wato jihar Kogi da irin cigaba da nasarorin da gwamnatin sa ta samu a tsawon mulkin sa, ya ce makiya da mahassada sun saka shi a gaba sannan sune ke juya kafafen yaɗa labarai a jihar.
” Ni fa ba zan ce muku komai ba game da irin nasarori da cigaba da muka samu a jihar Kogi, bukata ta ita ce duk mai son ya ga abin da muka yi yayi tattaki har jihar Kogi ya gai wa idon sa irin ayyukan da muka yi a jihar.
Yahaya Bello ya shiga sawun ƴan takara kamar su Rochas Okorocha, David Umahi, Bola Tinubu da dai sauransu waɗanda duka a jam’iyyar APC suka fito takarar shugaban kasa.