Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa a fafutikar da ya ke yi na neman zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023, tuni ya rigaya ya samu ƙuri’u miliyan 11 tun ma kafin zaɓen ya zo nan da shekara ɗaya.
Ya ce wannan da ɗaya daga cikin dalilan da su ka sa ya fi cancanta jam’iyyar PDP ta ba shi takarar shugabanci kawai, ba sauran ‘yan takarar PDP ɗin ba.
Atiku ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da ya ziyarci Shugabannin Kwamitin Gudanarwar PDP a Abuja, domin neman goyon bayan su.
“Ni ne fa gayen da tun tuni har ma na rigaya na samu ƙuri’u miliyan 11. Saboda haka ina ganin kawai Ni ya kamata ku bai wa takara, domin PDP ta yi amfani da ƙuri’u na ta ƙarasa cin zaɓe a wuce wurin.”
Haka Atiku ya furta a lokaci ɗaya kuma ya na dukan ƙirjin sa, yayin da ɗimbin magoya bayan sa suka cika zauren taron da sowa da tafi da jinjina ga Atiku.
An dai gudanar da taron ganawar a hedikwatar PDP da ke Wadata Plaza, Abuja.
Atiku ya yi wannan iƙirarin samun ƙuri’u kwana biyu bayan wasu magoya bayan ɗan takarar APC, Bola Tinubu sun yi iƙirarin cewa sun tanadar wa Tinubu ɗin ƙuri’u miliyan 14 a yankin Kudu maso Yamma, yankin da Tinubu ya fito.
Duk da cewa Atiku Abubakar ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari a zaɓen 2019, ya samu ƙuri’u miliyan 11 a zaɓen na 2019. Sai dai kuma ba a sani ba ko waɗannan ƙuri’un Atiku ke nufi, ko kuma wasu daban.
Rahotanni da ƙididdigar ƙuri’un zaɓukan da suka gudana a baya sun nuna ana ci gaba da ƙaurace wa zaɓe a Najeriya.
Shi dai Atiku ya ce jam’iyyar PDP ce ke da “ɗan takarar da ya fi cancanta ya samar da shugabanci nagari a ƙasar nan.”
Daga nan sai ya ce, “don haka Ni ne ɗan takarar da ya fi cancanta.”
Ya kuma roƙi Kwamitin PDP ya yi adalci wajen fitar da wanda ya fi dacewa ya tsaya wa PDP takarar zaɓen 2023.
Atiku ya maimaita ajandar sa idan ya zama shugaban ƙasa, waɗanda suka haɗa da haɗa kan Najeriya, farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, daƙile matsalolin tsaro da sauran su.