Bulalar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Kalu wanda ke neman fitowa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, ya yi tir da duk wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya fito daga Kudu-maso-yamma da na Kudu-maso-kudu.
Ya ce tunda ba su ganin daraja da mutuncin yankin Kudu-maso-gabas, ballantana har su yi adalci su bar wa yankin takarar shugaban ƙasa, to shi zai janye daga shiga takarar.
Haka Kalu ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Kalu bai ware ɗan takarar APC ko PDP ba, ya ce kamata ya yi su mutunta haƙƙin zamantakewa duk su janye su bar wa ɗan ƙabilar Igbo ya fito takarar shugabancin ƙasar nan.
Idan ba a manta ba, a farkon wannan watan ne Kalu ya ce zai fito takara a ƙarƙashin APC, idan har aka bar wa ‘yan ƙabilar Igbo su yi shugabancin Najeriya cikin 2023.
Ya zargi ‘yan takarar da su ka fito daga kudu da yi wa ƙabilar Igbo rashin adalci.
Kalu ya daɗe ya na kakabin neman a yi adalci a bar ‘yan ƙabilar Igbo su yi takarar shugabancin ƙasa a 2023 a tsakanin su.
Kalu ya ce duk da ya na son tsayawa takarar shugabancin Najeriya, to ba zai iya ƙaddamar da takarar sa, ba tare da goyon bayan yankin Kudu-maso-kudu da Kudu-maso-yamma ba.
Saboda haka ne ya ce ba shi da zaɓi, sai dai ya “koma Majalisar Dattawa, ya nesanta kan sa daga zaɓen shugaban ƙasa ko takarar zaɓen.”
“Ina mamakin ganin yadda ‘yan takara suka fito birjik daga Kudu-maso-yamma da Kudu-maso-kudu daga ɓangare biyu, wato APC da PDP. Abin kunya ne sosai, ganin yadda ba su ko ganin kima ko mutuncin yankin Kudu-maso-gabas, wanda bai taɓa samar da shugaban ƙasa mai cikakken ikon dimokraɗiyya ba.
“Na yi tunanin za su tuna da mu su goya mana baya, ɗan Kudu-maso-gabas ya yi shugabanci a 2023. Amma idanun su sun rufe, sai bindiga suke ta yi da kuɗi. Sun manta kuɗi ba ya sayen kujerar shugaban ƙasa.”