Ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP, Peter Obi, ya ce ‘yan Najeriya su daina nema ko yardar wata jam’iyya ta tsayar da ɗan takara ta hanyar cimma yarjejeniyar a janye masa, abin da a Turance ake kira ‘concensus candidate’.
Obi wanda ya yi takarar matsayin mataimakin shugaban ƙasa a PDP lokacin zaɓen 2019, ya ce a yanzu Najeriya na buƙatar dan takarar da zai fitar da ƙasar daga ɗimbin matsalolin da su ka dabaibaye ta.
Haka dai ya bayyana harin Abakaliki a ranar Talata, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai.
Obi ya kai ziyarar tuntuɓa ce ga masu ruwa da tsaki na PDP a Jihar Ebonyi.
“Abin da Najeriya ke buƙata a zaɓen 2023 shi ne shugaban ƙasa wanda da zarar ya hau mulki ya fara aikin warware ɗimbin matsalolin da suka dabaibaye ƙasar nan.
“Su na buƙatar wanda zai kare rayukan su da dukiyoyin, ya farfaɗo da arzikin arzikin ƙasar nan, ya ceto talakawa daga cikin kogin ƙuncin rayuwa, talauci da fatara.
“Batun shugaban da za a zaɓa ba magana ba ce ta wakilan zaɓe, wato ‘deligates’ saboda ko su yankin da ya fi kowane yanki yawan wakilai da su kan su wakilan, a cikin waɗannan matsalolin su ke tsundum.
Yayin da Obi ya fito takarar shugabancin ƙasa, zai kafsa ne a ƙarƙashin PDP tare da Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal, Nysome Wike da sauran manema takara masu yawa a PDP.
Ya ce a yanzu da ƙasar nan ke cikin wani mawuyacin hali, maganar a fito da ɗan takara ta hanyar cimma yarjejeniyar janye wa mutum ɗaya bai taso ba. Cewa ya ce duk wanda zai iya fitar da ƙasar nan daga matsaloli, to shi ya kamata a zaɓa.
Daga nan ya riƙa nuna cancantar sa zama shugaban ƙasa, ya na tunatar irin masaniyar sa da zurfin hada-hadar sa a kasuwanci da tattalin arziki.
“Haka batun shiyya-shiyya ma yanzu bai taso ba. Ko ma daga ina ɗan takarar zai fito, idan dai wanda za iya ceto ƙasar nan, to shi Najeriya ke buƙata.
Idan za a tuna, PREMIUM TIMES Hausa ta sha buga labarin ƙoƙarin cimma yarjejeniyar janye wa ɗan takara ɗaya da wasu ‘yan takarar PDP ke yi.
Masu wannan ra’ayin sun haɗa da Bukola Saraki, Aminu Tambuwal da Bala Mohammed.
Matsalolin Najeriya: Ninancin Peter Obi:
Peter Obi bayan ya gama dogon jawabin sa, ya bayyana cewa shi ne zai iya ceto ƙasar nan da kuma ceto tattalin arzikin ta.
“Zan iya ceto ƙasar nan, domin ina da rekod da ƙwarewa, kasancewa tun da farko na fara da zama ɗan tireda, na yi hada-hada a cikin duniya a manyan kamfanonin da ake tinƙaho da su, kuma na yi gwamna.” Inji shi.