Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyun siyasa cewa kada wadda ta kuskura ta kawo wa tsare-tsare da matakan shirya Zaɓen 2023 tarnaƙi ko yunƙurin gurgunta shirin.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran INEC ya fitar a ranar Talata, INEC ta ce ba za ta lamunci duk wani yunƙurin da wata jam’iyya ko jam’iyyu za su yi ba, wajen kaucewa ko yin biris da dokokin zaɓen da Kundin Dokokin Najeriya ya shimfiɗa ba.
Musamman INEC ta yi gargaɗin ne dangane da batutuwan tsayar da ‘yan takarar zaɓen fitar-da-gwani a na kowace jam’iyya.
Tun ranar da INEC ta canja ranakun gudanar da zaɓuka a cikin watan Fabrairu, kuma ta fito da shirye-shirye da ranakun gudanar da ayyukan ta, har yanzu ayyuka biyu daga cikin tsare-tsaren hukumar guda 14 ta cimma nasarar aiwatarwa.
Tsare-tsaren guda biyu kuwa su ne buga sanarwar ranakun zaɓe a jihohi da fitar da fam na ‘yan takara, wanda ya a fitar a shafin hukumar na yanar gizo.
Kamar yadda Sashe na 84 na Dokar Zaɓe ya tanadar, dukkan jam’iyyu na da wa’adin kwanaki 61 ne, wato daga 4 Ga Afrilu zuwa 3 Ga Yuni, domin su fitar da ‘yan takarar zaɓukan shugaban ƙasa, gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da na ƙasa waɗanda za su yi takara a zaɓen 2023.
Yayin da INEC ta aza ranar 25 Ga Fabrairu, 2023 za ta yi zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dattawa da na Tarayya, su kuma zaɓukan gwamna da na ‘yan majalisar Dokoki za a gudanar da shi ne a ranar 11 Ga Maris.
Ƙa’idojin Fidda Ɗan Takarar Zaɓen 2023 -INEC:
“Tilas a kasance ƙa’idar da za a bi wajen fitar da ɗan takara a dukkan mazaɓu 1,491 na ƙasar nan, a kasance kuma a tabbatar an gudanar da zaɓen fidda gwani sahihi, a fili ba nuƙu-nuƙu, kamar yadda Sashe na 29 da na 84 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya shimfiɗa.”
“Duk inda wata jam’iyyar siyasa ta kasa ko da gangan ta ƙi bin waɗannan sharuɗɗa wajen gudanar da zaɓen-fidda-gwani, to INEC ba za ta sa sunan ɗan takarar ta a zaɓe a muƙamin da ya ke takara ba.
“Kamar yadda doka ta buƙata, INEC za ta sa-ido a dukkan zaɓukan fidda gwani domin gane wa idon ta yadda lamarin ke tafiya. Kuma doka ta ce jam’iyyar ce da kan ta za ta sanar wa INEC ranar da za ta yi zaɓen fidda gwani, domin ta je ta sa-ido.
“Duk jam’iyyar da ta ƙi sanar wa INEC ranar da za ta yi zaɓen fidda gwani, ko taron gangamin jam’iyya domin fitar da ɗan takara, to zaɓen na ta ko taron gangamin ya tashi a tutar banza, ɗan takarar da aka fitar ba zai shiga zaɓe ba.
“Tilas ya kasance an yi zaɓen fidda gwani a cikin mazaɓar da doka ta tanadar, ba wani wuri can daban ba. Saboda INEC ba za ta amince da ɗan takarar da aka fitar ba a mazaɓar da ya kamata a fitar da shi aka yi zaɓen ba.
Ƙa’idar Cimma Yarjejeniyar Tsayar Ɗan Takara Ba Ta Hanyar Zaɓe Ba:
Akwai hurumin amincewa a tsaida ɗan takara ta hanyar cimma yarjejeniyar amincewa a tsayar da wani daga cikin ‘yan takarar ba tare da an yi zaɓen fidda gwani ba.