Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose, ya bayyana cewa idan ya ci zaɓen shugaban ƙasa, zai naɗa “Ministan Cika Cikin Talakawa da Abinci”
Fayose ya bayyana haka yayin da ya ke magana da manema labarai, jim kaɗan bayan ya fito zauren tantance ‘yan takarar PDP, ranar Juma’a, a Abuja.
Kwamitin Tantance ‘Yan Takara da ke ƙarƙashin shugabancin Sanata David Mark, sun tantance ‘yan takara 17, amma an soke biyu.
A lokacin da kwamiti ta tambayi shi neman ƙarin harke a kan shirin Cika Cikin Talakawa da Abinci, wanda ya yi a lokacin ya na gwamna, Tsohon Gwamnan nan Ekiti ya amsa da cewa idan ya zama shugaban ƙasa sai bijiro da shirin, ta yadda zai zama na ƙasa baki ɗaya.
“Na shaida masu cewa zan naɗa Ministan Cika Cikin Talakawa da Abinci kuma zan samar wa talakawa walwala da jin daɗi.” Inji Fayose.
Ya ce matuƙar cikin talakawa na yini su na kuma kwana da yunwa, to talaka ba zai taɓa ganin gina kwalta da sauran ayyukan raya ƙasa da muhimmanci ba, duk kuwa da irin muhimmancin da suke da shi.
“Saboda haka a gani na shirin ciyar da talakawa na ɗaya daga cikin shirye-shiryen tallafa wa talaka. Kuma idan na zama shugaban ƙasa, zan bai wa shirin muhimmanci sosai.
Da Fayose ya ke magana a kan tsarin karɓa-karɓa, ya ce ya zama wajibi PDP ta yi tsarin karɓa-karɓa da tikitin takarar shugaban ƙasa, gudun kada nan gaba lamarin ya ruɗe mata.
Ya ce idan ma PDP na so kowa ya fito takara, to ta dai fito ta bayyana cewa ta bayar da tikitin takarar shugaban ƙasa ga kudancin Najeriya.
Ya tunatar cewa a 1999 PDP ta bayar ta takarar shugaban ƙasa ga kudu, inda Obasanjo da Olu Falae su ka tsaya takarar fidda-gwani. Amma duk da haka sai da marigayi Abubakar Rimi ya fito takara, kamar yadda dokar ƙasa ta ba shi haƙƙin fitowa, idan zai iya.
“To amma dai PDP ta sani cewa duk abin da muka yi a yanzu, zai amfane mu ko ya zame mana alaƙaƙai nan gaba.
“Saboda tsarin ƙasar mu da tubali da ginshiƙin gina mulki ba daidai su ke a girke ko tsarin ke tafiya ba, shi ya sa mu ke ta fuskantar waɗannan matsalolin.
“Ya kamata mu yi ƙarfin hali mu fito mu ce a miƙa takara ga kudu, amma duk mai sha’awa zai iya fitowa takara kamar yadda dokar Najeriya ta bayar da haƙƙi. Amma dai Ni wannan lokacin na goyi bayan a bai wa kudu takara kawai.”
Fayose ya ce tunda shugaban yanzu da zai sauka bayan ya shafe shekaru takwas ɗan Arewa ne, to abin da kawai ke daidai shi ne shugaban da za a zaɓa a 2023 ya fito daga kudu, ko ma a wace jam’iyya zai fito.
“Wannan batu ba na jam’iyya ba ne, magana ce ta jaddada adalcin haƙƙin zamantakewar al’umma tare domin samun zaman lafiya da dawwamammen kwanciyar hankali.”