Gwamnonin Yankin Kudu ‘yan jam’iyyar PDP sun sake jaddada cewa tilas sai dai a bayar da takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2023 ga ɗan yankin Kudu.
Sun ce a haka ne kawai za a tabbatar da adalci a siyasa, mulki da zamantakewar tare a Najeriya.
Gwamnonin sun bayyana wannan matsaya ta su a lokacin da su ke wa manema labarai jawabi, ranar Juma’a, a Gidan Gwamnatin Jihar Akwa Ibom da ke Asokoro, Abuja.
Gwamnan Jihar Abiya Okezie Ikpeazu ne ya yi wa manema labarai jawabi a madadin sauran gwamnonin.
Ya ce su na lura da duk irin karankaɗakaliyar siyasar neman mulki daga ɓangarori a ƙarƙashin PDP, musamman tayar da jijiyoyi kan karɓa-karɓa. A gaskiya babu wani dalili da zai sa su canja yarjejeniyar karɓa-karɓa
“Matsayar mu ita ce, na farko mu na masu nuna goyon baya da jam’iyyar mu. Mun kuma yi amanna da cewa sun ƙarfin jam’iyyar mu idan muka dunƙule, muka fuskanci zaɓen 2023, to za mu yi nasara.
“Amma kuma a Delta da Bayelsa mun amince tare da yin riƙo da cewa tilas fa a mutunta yarjejeniyar karɓa-karɓa, a bar wa Kudu ta fitar da ɗan takarar PDP a shugabancin ƙasar nan. Kuma a wannan matsayin mu ke nan.”
“Ba mu ga dalilin da zai sa a canja tsarin yadda aka taho tun farko ba. ”
Da aka tambaye shi me za su yi idan aka bar takarar a buɗe aka ce kowa ma ya fito, sai Ikpeazu ya ce, “kai kuma ba ka faɗa min dalilin za zai sa ba za mu yi nasarar zaɓen 2023 idan aka bai wa ɗan Kudu takara a bisa tsarin karɓa-karɓa ba.”
Kan batun Kwamitin PDP ya rushe batun karɓa-karba, sai Ikpeazu ya ce ai su gwamnonin PDP na Kudu ba su aiki da ji-ta-ji-ta.
Wannan jarida ta buga labarin yadda makonni biyu da suka gabata, gwamnoni da jiga-jigan kudu suka ce tilas fa sai ɗan Kudu zai zama shugaban ƙasa -Dattawan Kudu-maso-kudu, ‘yan PDP.
Shugabannin PDP na Reshen Kudu maso Kudu, sun ce babu ruwan su da wani ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP daga Arewa, su sai fa ɗan kudu ne kaɗai su ka amince ya yi shugabanci a zaɓen 2023.
Wannan buƙata ta su na cikin wata sanarwar bayan taro da su ka fitar na shugabannin PDP na yankin Jihohin Ƙabilun Kudu maso Kudu. Sun yi wannan taro ne ranar Litinin a Uyo.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso Kudu kuma Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, shi da Gwamna Nysom Wike na Ribas har ma da Udom Emmanuel na Akwa Ibom duk sun halarci taron. Haka ma Gwamna Douye Diri na Bayelsa, shi ma ya halarta.
“Wannan Shiyya ta Kudu maso Kudu na goyon bayan matsayar Gwamnonin Kudu cewa sai fa ɗan Kudu ne zai yi shugaban ƙasa a zaɓen 2023.” Haka dai shugabannin su ka ƙara jaddadawa.
Gwamna Okowa ya ce jam’iyyar PDP na da “ƙudirin da ta ke son ta cimma” na ceto Najeriya daga jam’iyyar APC. Sannan kuma ya yi kira ga PDP ta kasance cikin haɗin kai domin a ci gaba da tafiya tare daga nan har zaɓen 2023.
“Mun yi amanna cewa nan da watan Fabrairu 2023, za mu samu gagarimar nasarar lashe zaɓe, mu ceto Najeriya.”
Haka ya furta a wurin taron wanda mambobin Majalisar Tarayya na Kudu Maso Kudu suka halarta tare da shugabannin PDP na shiyya.
Shi kuwa Gwamna Wike cewa ya yi PDP a yanzu ta na da damar karɓe mulki ta hanyar zaɓe daga hannun APC. Don haka ya ja hankalin cewa kada a yi wasa ko wasarere da wannan dama ta suɓuce.
“Yan Najeriya na jiran PDP ta amshi mulki kawai a zaɓen 2023. Amma fa hakan ba zai yiwu ba idan ba mu haɗa kan mu ba, kuma mun yi aiki tare.”
Gwamna Emmanuel cewa ya yi PDP cewa ya yi jam’iyyar PDP ce kaɗai ke iya farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan daga halin ƙuncin da ‘yan ƙasar ke fama da shi da kuma gurguntakar tattalin arziki.
Daga nan shugabannin PDP sun nuna damuwa kan yadda har yanzu Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta (NDDC) har yanzu ta ke a hannun Kantoman Riƙo. Daga nan su ka ce wannan an karya dokar NDDC, kuma su ka nemi a kafa Hukumar Gudanarwar NDDC ba tare da ci gaba da ɓata lokaci ba.
A ƙarshe sun kuma nemi a fito da sakamakon binciken badaƙalar cin kuɗaɗen NDDC domin kowa ya gani.