Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cewa zaɓen shi da Sanata Bukola Saraki da Dattawan Arewa suka yi, a matsayin su ne ‘yan takarar da Arewa za ta tsayar a zaɓen fidda gwanin PDP, nufi ne na Allah, amma ba wani matsin-lambar su ba ne.
Wannan jaridar ta buga labarin da ya ruwaito daga Vanguard cewa Dattiɓan Arewa sun fitar da Sanata Bukola Saraki da Gwamna Bala Mohammed a matsayin ‘yan takarar da Arewa za ta tsayar wajen zaɓen fitar da gwanin PDP, a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Shi ma Tambuwal ya yi fatali da rahoton da Ango Abdullahi ya ce sun zaɓi Saraki da Bala a matsayin waɗanda za su kafsa wa ‘yan takarar da za su fito daga Kudu.
Wani ɗan takarar mai suna Hayatuddeen shi ma ya ƙi yarda da yarjejeniyar da Ango Abdullahi ya ce Dattawan Arewa ta cimmawa.
Amma shi Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya ce duk da bai ma san an tsayar da su ɗin ba, to hakan da aka yi lamari ne daga Allah.
Bala ya gode wa Ƙungiyar Dattawan Arewa, kuma ya ce sun yi hangen nesa da zurfin tunani da suka zaɓi waɗanda su ka cancanta
“Za mu ɗauki wannan a matsayin wani nauyi da aka ɗora mana. Kuma za mu gayyaci sauran ‘yan takara, domin a tafi tare. Sannan kuma za mu yi ƙoƙarin ganin an kauce wa rabuwar kawuna, husuma da yankan-baya.”
Premium Times Husa ta buga labarin da Suke Lamiɗo ya ce PDP ba ta tsamo Saraki da Balan Bauchi ta ce su ne ‘yan takarar Arewa ba.
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya ƙaryata rahoton da ya ce Dattawan Arewa da ‘yan takarar PDP na shugabancin ƙasa sun zaɓi tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi a matsayin ‘yan takarar da Arewa za ta tura wakilci a zaɓen fidda-gwanin PDP.
Jaridar Vanguard ce dai ta buga labarin cewa Dattawan Arewa sun tsayar da Saraki da Bala Mohammed ‘yan takarar su na zaɓen fidda-gwani wanda za a yi a ranar 28 Ga Mayu, 2022.
Jaridar ta ce wannan matsaya da suka ɗauka na ƙunshe cikin wata takardar bayan taro da dattijo Ango Abdullahi ya sa wa hannu, cewar Vanguard.
Sanarwar ta ce Dattawan Arewa ɗin sun zaɓi ‘yan takarar biyu daga cikin huɗun da suka miƙa sunayen su domin tantancewa.