Ɗan shugaban cocin ‘Redeemed Christian Church of God (RCCG) Enoch Adeboye kuma fasto a cocin Leke Adeboye ya nemi afuwar fastocin dake wa’azi a cocin mahaifinsa da ya kira su awakai.
“Ina so na yi amfani da wannan dama domin na nemi afuwan fastocin dake aiki a cocin RCCG da na kira su awakai a shafi na na Instagram dake yanar gizo.
“Ina rokon gafarar su bisa ga abin da na rubuta domin na rubuta shi ba da nufin na bata wani ko na zagi wani ba.
Kafin hakan ya faru Adeboye ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa duk fastocin dake wa’azi a cocin mahaifinsa awakai ne.
A rubutun da ya yi Adeboye ya ce “A kan wani dalilin fasto zai tashi ya yi wa’azi bayan ‘Daddy GO’ ya kammala wa’azi?! Kai ba dabba bane amma akuya ne kai.
Rubutun da Adeboye ya yi ya jawo cecekuce daga mambobin cocin da sauran mutane a Najeriya.
Discussion about this post