Majiya dake kusa da iyalan babban manajan Bankin Ayyukan Gona, Alwan Ali-Hassan ya sanar da dawowar sa gida daga hannun ƴan bindiga.
Daily Nigerian ta buga cewa ɗan uwan Ali-Hassan sun biya kuɗin fansa kafin a ka sake sa.
Ali Hassan na daga cikin waɗanda ƴan bindiga suka yi awon gana da a harin jirgin kasa da suka kai a cikin makon jiya.
Gwamnatin Kaduna ta ce mutum 8 ƴan bindigan suka kasa sannan da yawa daga cikin matafin sun ji rauni.
Sannan maharan sun sace wasu da dam daga cikin matafiyan.
Discussion about this post