Ƴan bindiga sun kai wa wasu matsugunan fulani makiyaya hari a jihar Anambra.
Shugaban Miyetti Allah dake Obene, karamar hukumar Ogbaru, jihar Anambra ya bayyana wa manema labarai cewa ƴan bindigan sun kai wa Fulanin harin a cikin dare wajen karfe 1:30.
Ya ce sun kashe mutane sannan sun yi garkuwa da wasu mutum 10 sannan suka kaɗa shanu akalla 300.
Shugabam MACBAN na yankin kudu maso gabas Giɗaɗo siddiki ya ce kungiyar ta sanar da jami’an tsaro na ƴan sanda domin a ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga ya tabbatar da aukiwar abin amma kuma ya ce saboda karancin bayanai da suke da shi akan harin basu kai ga fara bincike akai ba.
” An kawo mana karar abin da ya auku, amma kuma ba mu da isassun bayanai akai. Mun umarci MACBAN su bamu isassun bayanai tunda har ƴan bindigan sun yi waya abiya kuɗin fansa naira miliyan 4.
Siddiki ya ce ƴan bindigan sun kira iyalan waɗanda suka yi garkuwa da su kuma sun buƙaci a biya su naira miliyan hudu kudin fansa.