Ƴan bindiga sun kashe ƴan kasuwa akalla 7 sannan sun yi garkuwa da wasu da dama a harin da suka kai kasuwar Ƴan tumaki, dake ƙaramar hukumar Ɗanmusa dake jihar Katsina.
Wani mazaunin garin Magaji Basiru ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ƴan bindigan sun afka cikin kasuwan da rana tsaka wajen ƙarfe 3.
Sun zo bisa babura goggoye da juna suka yi kan mai uwa dawabi da bindigoginsu.
Kakakin ƴan sandan Katsina Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar wannan hari inda ya kara da cewa a wajen gujeguje ne wasu yara biyu suka rasa ransu.
” Ƴan bindigan sun nausa kai tsaye ɓangaren masu saida wayoyin hannu ne. Sun kwashi wayoyi babu adadi sannan sun sace mutane da dama baya ga waɗanda suka kashe da kuma waɗanda suka ji rauni.