Babban Hafsan Sojojin Najeriya Faruk Yahaya, ya sake jaddada aniyar Rundunar Sojojin Najeriya ta ganin cewa wajibin su ne su murƙushe duk wasu masu kawo tashin hankali a faɗin ƙasar nan.
Laftanar Janar Yahaya ya bayar da wannan tabbacin a wurin wani taron da aka gudanar a Hedikwatar Ofishin Sojojin Najeriya a Abuja, ranar Talata.
Manjo Janar Anthony Omozoje Shugaban Sashen Tsare-tsare ne ya wakilci Faruk a wurin taron.
Ya ce yawaitar tashe-tashen hankula a ƙasar nan sun sa ana bibiya da canja takun tsarin daƙile bazazanar tsaro a kai a kai.
Ya ce ayyukan ‘yan ta”adda, masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga na ci gaba da kawo barazana ga ƙasar nan.
Ya ce barazanar ta kuma shafi har sojojin Najeriya.
Tun da farko dai Babban Jami’in Soja mai kula da fannin sufuri da ƙirƙira, Charles Ofoche ya ce taron kara wa juna ilmin da aka tsara, an yi shi ne domin a ƙara zaburar da dakarun da ke bakin fagen daga, kana gwabza yaƙi a Arewa maso Gabas da sauran yankunan da ake tashin hankula.
Faruk ya ce sojojin Najeriya na ƙoƙari sosai wajen gaggauta yi wa masu kai hare-hare dirar-mikiya.
Ya ce su na samun nasarori sosai, duk kuwa da irin ƙalubalen faɗaɗa da matsalar tsaro ke yi a yankuna daban-daban.
Idan ba a manta ba, Najeriya ta samu kan ta cikin gagarimar matsalar Boko Haram, yaƙin da ya gagari ‘yan sanda, sai dai ake amfani da sojoji fiye da shekaru 10.
Haka nan ma an zuba sojoji wajen ganin an daƙile hare-haren ‘yan bindiga, waɗanda su ma suka gagari ‘yan sanda.
Yamutsi da tayar da ƙayar bayan da tsagerun IPOB ke yi a Kudu maso Gabas shi ma ya yi munin da sai da Najeriya ta tura dakarun sojojin ta a yankin.