Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayar da gudunmawar naira miliyan 50 ga iyalan waɗanda harin jirgin ƙasa ya ritsa da su a dajin Kaduna.
NGF ta bayar da kuɗaɗen ne ga Gwamnatin Jihar Kaduna domin raba wa iyalan, kamar yadda wata sanarwa daga Jami’in Yaɗa Labarai na NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya fitar a Abuja, a ranar Juma’a.
Ya ce Shugaban Ƙungiyar ne kuma Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi ya bayar da gudunmawar, a lokacin da ya jagoranci tawagar mutum biyu zuwa Jihar Kaduna.
Fayemi ya shaida wa Gwamna Nasir El-Rufai cewa tawagar sa ta kai ziyarar ce a Kaduna, domin yin ta’aziyya, jaje da jimamin waɗanda aka kashe a harin, waɗanda aka ji wa raunuka da kuma waɗanda aka yi garkuwa da su a mummunan harin na ranar 28 Ga Maris.
Shugaban na NGF ya nuna tsantsar jimami da ta’aziyya ga iyalan waɗanda harin ya ritsa da su da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna.
“Abin takaici da tsananin ɓacin-rai shi ne yadda maharan har su ke da ƙarfin halin kwasar mutanen da su ka tsare, masu yawan haka.
“Wannan lamari ya ƙara ruruta ƙarfin matsalar tsaron da ake fama da ita a jihar Kaduna.”
Daga ya yi waswasin ko wannan gagarimar matsala wasu maƙiya Jihar Kaduna ko maƙiya gwamnan Kaduna ne ke da hannu a cikin ta, domin su karkatar da jihar daga gagarimin ci gaban da ta ke samu a yanzu.
“Saboda komai fa yanzu an jingina shi da lamarin 2023” a ƙasar nan.
Daga nan sai ya bayar da shawara a ƙara matsa ƙaimin tsaro a ɓangaren tsaro a ƙasar nan.
Ya ce a baya dai ba a san yankin Arewa maso Yamma da tashe-tashen hankula ba, sai a yanzu.
Bayan ya jaddada cewa gwamnonin Najeriya za su ci gaba da mara wa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari baya wajen ganin an magance tsaro, Fayemi ya kuma goyi bayan Gwamna El-Rufai wanda ke so ya ga sojoji sun bi ‘yan bindiga, sun yi masu takakkiya har maɓuyar su, sun dagargaje su.
Gwamna El-Rufai ya yi godiya, kuma ya shaida masa cewa a zaman yanzu akwai ‘yan jihar Kaduna mutum 61 da ke jiyya a asibiti, waɗanda harin jirgin ya ritsa da su. “Ciki har wa wani babban jami’in gwamnati da matar sa mai ciki wata 8.
Ya ƙara da cewa yanzu haka waɗanda su ka yi garkuwa da su, su na can cikin wani daji a Jihar Neja.
Ya yi takaicin faruwar lamarin, tare da cewa Hukumar Jiragen Ƙasa ta yi sakaci, domin sai da aka yi mata hannun-ka-mai-sanda kafin faduwar farmakin.
Discussion about this post