Fitowar Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2023 a ƙarƙashin APC, jam’iyya ɗaya da ubangidan sa Bola Tinubu, hakan ya nuna za a yi kokawa kenen tsakanin yaro da ubangida.
Akwai jan aiki sosai wurjanjan a gaban Osinbajo, wanda idan bai hana idanun sa barci ba, zai sha kayen tsiya a hannun Tinubu, ko dai da ƙarfin kuɗi, ko ƙarfin faɗa-a-ji, tunda Tinubu na da yara gwamnoni tsoffi da masu ci, tsoffin ministoci da waɗanda ke kan karaga, ko kuma ƙarfin ‘yan jagaliya.
Tashin farko za a ga cewa daga cikin gwamnonin APC 23, 12 kaɗai su ka halarci taron sa na ranar Lahadi, inda bayan an yi buɗa-baki ya bayyana masu niyyar sa ta fitowa takara.
Babbar matsalar da Osinbajo zai fuskanta kuma ita ce ta tsantsar ra’ayin sa na fifita mabiya Ɗariƙar ‘Pentacostal’, ‘yan Cocin RCCG a rabon muƙamai. Wannan halayyar ta sa na yi wa su kan su sauran Kiristoci ciwo.
Akasarin manyan muƙaman da Osinbajo ya yi hanya aka naɗa, duk mabiya Ɗariƙar da ya ke bi ne, ‘yan Cocin RCCG. Kakakin Yaɗa Labaran Osinbajo Laolu Akande, ɗan Cocin RCCG ne, kuma fasto ne a cocin na birnin New York, Amurka. Ya dawo Najeriya da aka ci zaɓen 2015, ya zama Kakakin Yaɗa Labaran Osinbajo.
A cikin Ministocin Buhari na 2015 zuwa 2019, Osinbajo ya bayar da sunan Okechukwu Enelameh aka naɗa shi Ministan Cinikayya, Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Jari (2015-2019). Shi ma fasto ne a Cocin RCCG.
RCCG na nufin Redeemed Christian Church of God.
Wasu ɓangaren Musulmi na jin haushin Osinbajo, ganin yadda a rayuwar sa Musulmai ne su ka cicciɓa shi har ya hau kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa, amma kuma sai ya riƙa maida hankali wajen naɗa ‘yan Ɗariƙar Cocin RCCG a manyan muƙaman gwamnati.
Osinbajo ya bayar da sunan faston RCCG, Babarunde Fowler aka naɗa shi Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga na Cikin Gida (FIRS), wanda ya shekara biyar sannan aka cire shi aka naɗa wani.
Musulmi Lauya kuma tsohon Ministan Shari’a, Bola Ajibola ne ubangidan Osinbajo na farko, kafin wani Musulmin, Bola Tinubu.
Kafin Tinubu, Yemi Osinbajo ya yi Hadimin Musamman a Ofishin Lauya na kamfanin Bola Ajibola.
Duk da ɗan asalin Jihar Ogun ne, hakan bai hana Bola Tinubu naɗa shi Kwamishinan Shari’a na Jihar Lagos ba, tsakanin 1999 zuwa 2007.
Kada a manta Osinbajo ya yi koyarwa a Jami’ar Legas.
Yayin da aka zo neman wanda za a naɗa Shugaban Hukumar BPE, an bai wa Osinbajo damar kawo wanda ya cancanta, inda ya bayar da sunan fasto Alex Ayoola-Okoh, ɗan Ɗarikar RCCG, ta su Osinbajo ɗin.
Haka Shuagaban Bankin Masana’antu (BOI), wanda Osinbajo ne sanadin naɗa shi, wato Olukayode Pitan, shi ma faston RCCG ne.
Ba waɗannan ne kaɗai ‘yan Cocin RCCG da Osinbajo ya yi wa hanya su ka samu manyan muƙamai ba.
Kada kuma a manta, a cikin 2016, watan Nuwamba, jaridar Vanguard ta ruwaito Osinbajo na cewa, “Tinubu ne ya bada suna na aka naɗa ni ɗan Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa a APC.”
Ko ma dai me kenan, alamomi sun nuna cewa Osinbajo ya fara gane cewa waɗannan halayyar da ya nuna a baya za su iya zame masa matsala a zaɓe ko a zaɓen fidda gwani. Ba mamaki mai yiwuwa dalili kenan ya fara jawo Musulmai a jika, ta hanyar ɗaukar nauyin tafsirin watan azumi a wasu gidajen radiyo.
Sannan kuma kiran gwamnonin APC taron shan ruwa a ranar Lahadi da ta gabata, shi ma wata hanya ce ta fara sakin ra’ayin sa na riƙau kan Ɗarikar RCCG.
Shi ma ubangidan sa Tinubu akwai ƙalubalen matsalolin da zai fuskanta sosai. Na farko farfagandar cewa tsoho ne tukub ta yi mummunan tasiri a ƙoƙarin sa na neman a tsaida shi takara a APC.
Masu amfani da wannan farfaganda na cewa kada wani tsoho ya sauka, kuma a maye gurbin sa da wani tsohon.
Sannan kuma an riƙa yaɗa cewa shi ma ko ya hau, a Landan zai riƙa zirga-zirgar fita neman magani ko ganin likitocin sa, ya na farin ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Matsalar motoci biyu masu sulke ɗauke da maƙudan kuɗaɗe a jajibirin zaɓen 2019 daga banki har cikin gidan Tinubu, ta sa an riƙa tanganta shi tamkar wani samfurin maguɗin zaɓe.
Kari da cewa ana raɗe-raɗin zai ɗauki Gwamna Abdullahi na Jihar Kano a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, ya sa Tinubu ba zai iya yin tasiri a Arewa ba, sai dai idan ƙarfa-ƙarfa ko hajijiya za a yi ranar zaɓe.
Ana yi wa Ganduje kallon wanda ya yi ƙarfa-ƙarfar cin zaɓe a 2019 a ‘incoclusive’ na Mazaɓar Gama, cikin Ƙaramar Hukumar Nasarawa.
Sannan kuma bidiyon da ake zargin ya na danna dalolin toshiyar baki a cikin aljifan sa, har yau ba su fice daga ƙwaƙwalen ɗimbin jama’a ba, duk kuwa da an raɗa wa Ganduje suna Khadimul Islam.
Kada a yi mamakin kokawar neman takara tsakanin Tinubu da Osinbajo. Mulki ya gaji har ɗa ya yi wa uban sa juyin mulki. Hakan ba sabon abu ba ne. Ballantana kuma kokawar yaro da ubangida.
Ai dama Bahaushe ya ce, “na kawo ƙarfi ya fi wane ya girme ni.”
Discussion about this post