Gungun wasu riƙaƙƙun masu garkuwa da mutane, waɗanda su ka addabi garuruwan yankin Kano da Jigawa sun yi saranda ga ‘yan sandan Jigawa. Haka dai mahukunta a jihar su ka bayyana.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, Lawan Adam ya bayyana cewa Eriya Kwamandan ‘Yan Sandan Ringim ne MK Abdullahi ya riƙa bibiyar su, kuma ya ribbace su har su ka amince su ka yi saranda, tare da makaman su.
Adam ya ce masu garkuwar su na ƙarƙashin jagorancin shugaban su mai suna Yusuf Wakili, mai shekaru 30.
Yusuf ɗan asalin yankin Ƙaramar Hukumar Ajingi ta Jihar Kano ne, ya damƙa wa ‘yan sanda bindiga ɗaya samfurin AK 47 da kuma ƙananan bindigogi biyu.
“A ranar 26 Ga Maris, 2022 ne Eriya Kwamandan Yankin Ringim, ACP M K Abdullahi ya samu rahoton sirri, wanda ya yi sanadin ya ja hankalin ɗaya daga cikin ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, Yusuf Wakili, wanda ake yi wa laƙabi da Rago ‘m’, mai shekaru 30, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Ajingi ta Jihar Kano.
“Ya miƙa wuya yayi saranda tare da sauran abokan yin garkuwar sa su huɗu, Inusa Jibril, Tahir Zango, dukkan su ‘yan Ajingi. Sai Sabo Abdullahi da ake kira Sabo Gara, ɗan Ƙaramar Hukumar Ringim da ke yankin Gerawa.
“Akwai kuma Suleiman Garba da ake kira Manu Dogo, mazaunin Wangara a Ƙaramar Hukumar Dutse ta Jihar Jigawa.”
Waɗanda suka miƙa wuyan dai ana zargin su da yawan aikata garkuwa da mutane da fashi da makami a yankunan jihohin Kano da Jigawa.
Adam ya ce an maida su Babban Sashen Binciken Manyan Laifuka na ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, inda ake masu tambayoyi.
Ya ce su na bada haɗin kai sosai, domin ƙoƙarin gano sauran abokan aikata garkuwar ta su.
Za a gurfanar da su a kotu, da zarar an kammala bincike.