Wasu daga cikin jigajigan jam’iyyar PDP da suka hada da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, Sanata Philip Aduda, tsohon gwamna Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose sun kai ziyarar zawarcin sanata Danjuma Goje ya dawo jam’iyyar PDP.
Goje yayi minista, sannan yayi gwamnan jihar Gwambe daga 2003 zuwa 2011. Daga nan sai ya zarce majalisar Dattawa wanda har yanzu yake a kai.
Majiya ta ce waɗannan gaggan ƴan siyasa sun ziyarci Goje domin zawarcin sa ya dawo jam’iyyar PDP wacce dama daga ita ce ya koma APC a 2015.
Koda yake ganawar sun yi sa ne a asirce amma majiya mai tushe ta shaida cewa lallai magana ce ta siyasa ya kawo wurin sanata Goje kuma zawarcin sa suke yi domin ya dawo jam’iyyar PDP a buga da shi
Idan ba a manta ba Sanata Goje baya ga maciji da gwamnan jihar Gombe wanda ya mara wa baya a wanxan lokaci.
Masu yin fashin baki na ganin wannan wata dama ce da za a yi amfani da shi wajen karkato da ra’ayin sanatan ya dawo PDP a murza siyasar 2023 da shi.
Jam’iyyar PDP ta lashi takobin ganin duk wada za a yi wannan karon sai ta ga abin da ya ture wa buzu nada domin a shirye take ta dankara APC da kasa a zabukan da za a yi.