Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya roki ƴan takaran shugaban jam’iyyar APC da su daidaita a tsakanin su su fidda mutum ɗaya.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wajen taron ganawa da yayi da duka ƴan takaran shugaban jam’iyyar su 7 a fadar Aso Rock.
” Abinda na ke so shine mu haɗu dukkan mu haɗa kai maimakon ayi ta jani-in-jaka, a amince wa mutum ɗaya shikena ba tare da an fantsama zabe ba.
Bayan haka shigaban ya umarci jam’iyyar ta maida wa duk wanda ya janye kuɗin fom fin sa da ya.
Baya ga Abdulaziz Yari da ya yi wa tsarin jam’iyyar kunnen-uwar shegu yayi gaban kan sa duk da tsarin da akyi na ɗan yankin Arewa Ta tsakiya ne zai yi takaran shugaban Jam’iyyar, duka sauran yan yankin da jam’iyyar ta tsara ne.
Sanata Abdullahi Adama daga Jihar Nasarawa da Tanko Almakura na jihar ne ke kan gaba wajen yin nasara a zaben shugaban.
Bayan su akwai tsohon gwamnan Benuwai, George Akume, sannan kuma akwai Mohammed Eksu.
A wajen taron shugaban jam’iyyar Mala Buni, da sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa, Ibrahim Gambari.
Buhari ya umarci gwamnoni su tattara sunayen waɗanda suke ganin sune suka dacewa kuma aka yarda dasu gaba daya kawai a amince da su ba sai an kai ga yin zaɓe ba.