A cikin shekara hudu na lokacin mulkin siyasa, shekarar karshe tana zuwa da abubuwa kalakala. A bangaren masu mulki, idan suna da damar sake yin takara, tunaninsu zai tattara ne akan hanyar da za su koma kan kujerarsu. A bangaren yan siyasa masu zawarcin kujerun mulki kuwa, neman tikitin yin takara shine babbar gwagwarmaya tun kafin a zo maganar shiga zabe. A d’aya bangaren kuma, talaka mai gayya mai aiki yana gefe yana neman tasa mafitar shima.
A lokacin da mu ka shiga jajiberen shekarar zabe a Najeriya, ‘yan siyasa, masu mulki da marasa mulki, sun yi turus suna tunanin makomarsu. Duk da har yanzu ba a zo lokacin kamfen ba, yanzu lokaci ne na zawarcin tikitin tsayawa takara, amma duk da haka yan siyasa sun fara yin taron sirri da kungiyoyi da manyan mutane domin shirya gwadaben da zai kaisu wajen da su ka dosa.
To su kuma talakawa fa?
Wasu daga cikin talakawa sun yi karatun ta nutsu, saboda ba a cizon mu’umini sau biyu a rami d’aya inji Bahaushe. A yayin da wasu daga cikinsu su ka zauna akan wancan tsarin na baya. Kullum burinsu a shirya tafiyar da zasu samu kud’in cefane, daga baya ko me zai faru ya faru. Matasa masu ilimi daga cikin talakawa sun koma yiwa yan siyasa “scope” wanda da hausa za a iya fassarashi da “acuci gara.” Ma’anarsa ita ce, bayyana kai a matsayin masoya, bayan an samu abunda ake so sai a gudu wajen wani d’an takarar da siffa irin wacce aka bayyanawa kowanne d’an takara.
Siyasa ba bagidajiya bace, saidai talaka ya mayar da kansa bagidaje. Misali, duk sanda ku ka zabi d’an takara, daga baya ya juya muku baya, bayan ya cinye zangon mulkinsa na farko idan ya dawo muku ku ka karbeshi, sunanku gidadawa. Bagidaje shine mutumin da ba zai iya gane daidai ko rashin daidai ba saboda yana fama da cutar duhun kai.
Amfanin “tenure” a siyasa ita ce, bayar da damar shigarwa ko fitar da mai mulkin da ku ke so, ba ta da bambanci da kalmar “substitution” a filin wasa. Idan d’an wasa ya kasa yin kokari sai a cireshi don shigar da wanda ya fishi qwazo cikin wasan. Ga ‘yan takarkaru nan kamar jamfa a Jos sai fitowa su ke yi neman ofis din siyasa. Sai talaka ya yiwa kansa tunani sosai idan ba haka ba zai zama shagiri-girbau.
Allah ya jiyar da mu Alheri.