Idan Allah ya rayamu zuwa zaben 2023, watakila za a iya ganin siyasar da ba a ganta ba a baya, musamman matasa yan bana bakwai. A yayin da gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya zo karshen wa’adin mulkinsa na zango na biyu, alamu suna nuna cewa, za a iya samun tirjiya daga bangaren jigogin jam’iya idan tikitin takara ya je hannun wanda busu gamsu da shi ba. Wannan zai iya faruwa ne a bangarorin jam’iya mai ci, APC da kuma babbar jam’iyar adawa ta PDP.
A bangaren jam’iya mai mulki, akwai rikici a gaban kotun kokoli akan kujerar shugabancin jam’iyar a jiha tsakanin tsagin gwamnati da kuma tsagin tsohon gwamnan Kano kuma sanata mai ci, Malam Ibrahim Shekarau.

Alamu suna nuna cewa, komai zai iya faruwa a yayin da tsagin na Shekarau bu su ci nasara a kotun daga ita sai Allah ya isa ba. Wasu suna ganin kamar tsohon gwamnan da tawagarsa za su iya ficewa daga jam’iyar APC din zuwa PDP. A yayin da wasu su ke ganin hakan ba zai yiwu ba saboda rikicin da ya ke cikin ita kanta PDP din.
A bangare na babbar jam’iyar adawa din, akwai danbarwa tsakanin yan tsohuwar PDP, bangaren Ambassador Aminu Wali da kuma yan darikar Kwankwasiyya a karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. Wanda hakan zai wahala ya samar da matsaya a tsakaninsu saboda takarar mallakar jam’iyar a jihar Kano.
Wani masani mai suna Thomas Hobbes yace, idan mutane guda biyu su ka hadu akan son abu daya, to daga ranar sun zama makiyan junansu.
A kowanne bangare, akwai rikici akan wanda zai zama gwamnan Kano a zaben 2023. A tsagin gwamnati, akwai masoya da yawa, kuma kowanne yana jiran tikitin takara. Hakazalika, a bangaren jam’iyar PDP.
Wadanda su ka shahara a bangaren APC, akwai Murtala Sule Garo wanda sunansa ya shiga bakin mutane a baya, akwai Sanata Barau Jubrin daga tsagin su Shekarau, ga kuma mataimakin gwamna wanda ya koma gefe d’aya yana jiran ikon Allah.
Sannan akwai babban attajiri kuma mai budadden hannu, Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura wanda ya ke samun goyon baya. Bincike ya nuna Zaura a matsayin wanda ya ke jijiga jam’iyar APC a Kano. Sannan akwai attajiri Alhaji Inuwa Waya, wanda shima yana da karfi sosai.
A bangaren PDP kuwa, akwai bangaren tsohuwar PDP da su ke shirin fitar da dan takararsu. A yayin da Kwankwaso da mutanensa su ke shirin fitar da nasu dan takarar. A cikin Kwankwasiyyar ma an fara samun rikici. Wasu suna ganin Abba Kabir Yusif a matsayin dan takarar dole.
Misali, akwai wadanda ya dace su samu takarar kafin shi. Hakan ne ya sa ake ganin kamar su Dakta Yunusa Dangwani za su iya ficewa daga bangaren na Kwankwasiyya zuwa d’aya bangaren na PDP. A gefe daya kuma, akwai babban attajiri Dakta AB Baffa yana jiran tsuntsu daga sama gasashshe.
Rashin sanin makoma a jam’iyar tasu ne ya sa ake ganin Kwankwaso da mutanensa za su iya komawa sabuwar kungiyarsu mai suna NNPP mai kayan dadi. Shin hakan zai yiwu? Lokaci zai tabbatar da haka.
Allah ya sa mu ga alheri.
Discussion about this post