Zargi: Wani sakon da aka wallafa a shafin Tiwita na zargin wai za’a gama rajistan zabe ranar 22 ga watan Maris.
An kaddamar da rajistan wadanda suka cancanci kada kuri’a a zaben shekarar 2023 mai zuwa ranar litini 28 ga watan Yunin 2021. An yi wannan tanadin ne domin wadanda suka cancanci yin zaben amma ba su riga sun yi rajista ba.
Ranar laraba 2 ga watan Faburairu, wani mai amfani da shafin Tiwita mai suna Mo-Mo (@Moris_Monye) ya yi kira ga jama’a da su hanzarta su yi rajista domin za’a kammala yin rajistan ranar 22 ga watan Maris 2022.
Tantancewa
Mun fara da binciken da ya bayyana mana rahotanni daban-daban wadanda ke sanar da lokacin da aka kaddamar da rajistan zaben a watan Yunin 2021.
Misali a cewar rahoton jaridar The Cable, shugaban INEC Mahmood Yakubu ya ce “Daga ranar litini 28 ga watan Yuni 2021 za’a kaddamar da rajistan zabe a kasa baki daya, kuma za’a cigaba da yi har zuwa tsakiyar shekarar 2022.”
Wani rahoton da gidan talbijin na Channels ya shirya shi ma ya ce hukumar zaben za ta cigaba da gudanar da rajistan zaben na tsawon shekara guda, daga 28 ga watan Yuni, 2021.
Haka nan kuma bidiyon da Channels ya nuna ya gwado shugaban INEC Mahmood yana cewa, “za mu gudanar da wannan rajistan na tsawon akalla shekara guda.”
DUBAWA ta tuntubi kwamishinan hukumar zaben ta kasa, Festus Okoye da babban sakataren yada labaran shugaban INEC wato Rotimi Oyekanmi domin tantance wannan batu.
Mr Festus Okoye ya tura mana hoton jaddawalin shirin rajstan wanda aka kasa zuwa gida hudu, wanda kuma ya nuna cewa za’a kammala ranar 30 ga watan Yunin 2022.
An kaddamar da kashin farko daga 28 ga watan Yuni zuwa 21 ga watan Satumban 2021, na biyu kuma daga 4 ga watan Oktoba zuwa 30 ga watan Disemba, kashi na uku daga 3 ga watan Janairu zuwa 22 ga watan Maris sa’annan na hudu daga 11 ga watan Afrilu zuwa 20 ga watan Yunin 2022.
Mr Rotimi Oyekanmi, ya karyata zargin da cewa “ba za’a kammala rajistan zabe kafin karshen watan Yuni ba.”
A karshe
Zargin wai za’a kammala rajistan zabe ranar 22 ga watan Maris ba gaskiya ba ne. Jadawalin rajistan da hukumar zaben ta bayyana ya nuna cewa a karshen watan Yunin 2022 ne za’a kammala ba Maris ba.