Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa gwamnatin sa ta ɗauki rayukan ‘yan Najeriya da muhimmanci. Don haka a ko’ina su ke a duniya, za a kare rayukan su.
Buhari ya yi wannan bayani ne yayin da Najeriya ta fara kwaso ‘yan ƙasar daga Romaniya, bayan sun tsallaka can daga gudun kauce wa yaƙin Ukraniya da Rasha.
Kakakin Yaɗa Labarai na Buhari, Femi Adesina ya yi wannan sanarwa a ranar Juma’a, inda ya ce Buhari ya yi alwashin ne a ranar Alhamis a Nairobi, babban birnin Kenya, inda ya halarci taron UNEP50.
Ya yi bayanin yayin taron sa da ‘yan Najeriya mazauna Kenya.
“A ɓangaren mu, gwamnatin mu za ta ci gaba da bada fifikon kare rayukan ‘yan Najeriya a duk ƙasar da su ke zaune a duniya.
“Mun sha yi an gani, ba sau ɗaya ba mu na gaggauta ceto ‘yan Najeriya a Libiya, Afrika ta Kudu, kuma a yanzu ga shi mu na yi a Ukraniya, inda ake kwaso su daga Romaniya, inda dubban ‘yan Najeriya ke maƙale, su na jiran a kwaso su dalilin ɓarkewar yaƙin Rasha da Ukraniya.”
Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyema ne ya wakilci Buhari a wurin ganawa da ‘yan Najeriya a Nairobi ɗin.
Tuni dai Buhari ya dawo Najeriya tun a ranar Juma’a, inda bai zarce Landan jiyya ba, kamar yadda aka tsara lokacin tafiyar sa.
An dai tsara cewa daga Kenya Buhari zai zarce Landan ya shafe sati biyu.
Yayin da ya ke sanar da tabbacin dawowar Buhari, Kakakin sa Garba Shehu ya ce Buhari bai fasa zuwa Landan ba.
“Ya gama abin da ya je yi a Nairori, shi ya sa ya dawo domin ya ƙara shiri. Amma ranar Lahadi.”
Discussion about this post