Kwana ɗaya bayan an gaura wa matar tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano mari a wurin bukin saukar sa daga gwamna, tare da rantsar da sabon Gwamna Chukwuma Soludo, an gargaɗi Obiano cewa idan ya kuskura matar sa ta shiga siyasa, to za ta zubar masa da mutunci a ƙasar nan da duniya baki ɗaya.
Tsohon Shugaban Ndigbo reshen Jihar Anambra ne, Chris Emulano ya yi wannan gargaɗin a ranar Juma’a.
Ya ce Madam Obiano ta nuna ba ta da halin iya hulɗa da mutane, kuma ta na da zafin ran da bai kamata a ce ta wakilci jihar Anambra a Majalisar Dattawa ba.
“Irin yadda ta zubar da mutuncin ta, ta tsokani Bianca Ojukwu har aka gaura mata mari, hakan ya nuna ba za ta zama wakiliya ta ƙwarai ba, kuma bai ma kamata ta wakilci jihar Anambra ba.
“Obiano zai tafka kuskure idan ya bari matar sa ta shiga siyasa. Domin a yanzu ta na so ta fito takarar sanata. Amma zafin rai zai sa ta zubar da ƙimar ta da mutuncin mijin ta idan ta shiga siyasa.
Madam Obiano ta sha mari daga tsohuwar matar jagoran da ya kafa APGA, Odumegwu Ojukwu, a wurin rantsar da sabon Gwamna Charles Soludo, a Awka, a ranar Alhamis.
Wasu daga cikin abin da ya haɗa Madam Obiano faɗa da Bianca har ta sha kari a bainar jama’a, sun haɗa da tashin da ta yi ta je ta iske Bianca ta riƙa ɗura mata zagi ta na dangwalar mata kafaɗa ta yi mata baƙaƙen kalamai.
“Sai da ta kai ta kama min ɗankwali na wanda rawanin sarauta ne. Da na ga abin ya wuce gona da iri, bayan ni da na kusa da ni mun ce ta bari ta ƙi, sai na ɗaga hannu na wanke ta da mari, har garin ya yi mata duhu baƙi-ƙirin.”
Haka Bianca ta bayyana wa Gidan Talabijin na ARISE kuma ta buga a shafin ta na Tiwita da Facebook.
Dalilin da matar Ojukwu ta faska wa matar gwamna mari a taron saukar gwamna kan mulki.
Ba kamar yadda kafafen watsa labarai su ka riƙa watsawa a ranar Alhamis cewa matar gwamna mai barin gado na Anambra Willie Obiano ta taska wa Bianca Ojukwu mari ba, a gaskiyar lamarin shi ne matar Obiano ɗin ce aka dalla wa marin, ba ita ce ta yi marin ba.
Kafafen yaɗa labarai sun yi zaton Bianca aka mara, saboda ita aka je aka samu ta na zaune kan teburin ta a wurin taron rantsar da Charles Soludo Gwamnan Jihar Anambra, ranar Alhamis.
Bidiyo ya nuno Misis Obiano ta tashi daga kan kujerar ta ta je wurin Bianca Ojukwu. Yayin da aka ji ƙarar mari fafaaas!, sai aka yi tunanin Bianca da ke zaune ɗin ce aka mara. Amma bidiyo ya nuna cewa Bianca ɗin ce ta yi marin.
Wani gogaggen editan jarida da ke wurin, ya tabbatar da cewa Misis Obiano ta sha mari a wurin da mijin ta ya miƙa mulki aka rantsar da sabon gwamna, saboda ta je har gaban Bianca ta gaigaya mata magana.
“To ke da ki ke cewa har abada ba za mu yi gwamna ba, to mun yi ko ba mu yi ba?” Haka ɗan jaridar ya rubuta cewa Misis Obiano ta yi wa Bianca matar ɗan tawaye Ojukwu gori.
Jin haushin hakan ne ita kuma Bianca ta na zaune kawai sai ta ɗaga hannu ta gaura wa Misis Obiano mari. Daga nan jama’a su ka shiga tsakani.
Bianca Ojukwu ta daɗe ta na ragargazar Obiano da gwamnatin sa.
Bayan matar sa ta sha mari kuma, EFCC ta damƙe Willie Obiano yayin da ya ke shirin tserewa Amurka, bayan an gaggaura wa matar sa mari a wurin da ya damƙa wa Soludo mulki Jihar Anambra.
Jami’an EFCC sun ɗauki tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano cancak daga ofishin su na Shiyyar Legas zuwa Hedikwatar EFCC ta Abuja domin ci gaba da sharara masa tambayoyin salwantar maƙudan kuɗaɗe a lokacin mulkin sa.
Obiano zai sha tambayoyi bayan kuma an sharara wa matar da Misis Obiano mari a gaban jama’a, yayin da su ke miƙa mulki ga sabon Gwamnan Anambra, Charles Soludo.
EFCC ta kama Obiano a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Abuja, sa’o’i kaɗan bayan ya miƙa mulki a Enugu.
Ya garzaya Legas ne da nufin hawa jirgin sama zuwa Jihar Houston a Amurka, inda jirgi ke jiran sa.
Wannan rana ta zama baƙar rana ga Obiano, wanda a gaban sa kuma a gaban dubban jama’a, Bianca Ojukwu ta gaggaura wa matar sa mari wurin miƙa mulki.
Majiyar EFCC ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an damƙe Obiano wajen ƙarfe 8:30 na dare a ranar Laraba, kuma washegari Alhamis aka ɗauko shi a jirgi zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.
Har yanzu dai ba a san takamaiman ko naira biliyan nawa EFCC ke ƙoƙarin ganin Obiano ya amayas ba.
Sai dai kuma idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labari ƙarshen 2021 cewa Hukumar EFCC ta rubuta wa Hukumar Shige da Fice Wasiƙa a ranar 15 Ga Nuwamba cewa su sa ido kan Obiano duk inda zai fita daga ƙasar nan. Su kula da ranar da zai fita ko ranar dawowar sa.
EFCC ta kama shi sa’o’i kaɗan bayan ya rasa rigar sulken kariya a lokacin ya na gwamna, rigar da ke hana duk irin ɓarnar da gwamna ya yi, ya fi ƙarfin kamu, sai dai a jira bayan saukar sa.