Gwamna Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto da ke neman a tsaida shi takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP, ya gargaɗi ‘yan Najeriya cewa kada a yi saki-na-dafen sake zaɓen dattijon duk da ya cimma shekaru 60 abin da ya yi sama a matsayin shugaban ƙasa, a zaɓen 2023.
A yanzu dai Tambuwal shekarun sa 56 da haihuwa, kuma ya dage bakin ƙoƙarin sa ya na son ganin cewa PDP shi ta tsayar, ba Atiku Abubakar ko wani ba.
Tambuwal ya yi wannan bayani a Jihar Jigawa, bayan da Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) na Jihohin Arewa 19 su ka yi masa mubaya’a, su ka ce shi ne ɗan takarar su.
Kwamishinan Harkokin Matasa da Wasanni na Jihar Sokoto, Bashir Usman ne ya wakilci Tambuwal a taron.
“Matasan Najeriya su ke da ƙasar nan. Duk wanda ya haura shekaru 60 a duniya, shure-shuren ƙarasawa ya tarad da mahaliccin sa kawai ya ke yi amma ba motsa jikin ƙarin ƙarfin iya shugabancin ƙasa ya ke ba.” Inji Tambuwal a wurin taron.
“Mu na buƙatar shugaban ƙasa mai lafiya ƙalau. Mai ƙarfi gagau, mai kuzari garau. Kuma mai jimirin kazar-kazar da gwarin-guiwar jure gaganiyar shugabancin al’umma kamar Najeriya.
“Mu na buƙatar lafiyayyen shugaba wanda zai iya kewaye Najeriya ɗaya rana domin ya gani kuma ya ji dukkan abubuwan da ke faruwa ko su ke addabar ‘yan Najeriya. Amma ba wanda kawai zai zauna cikin ofis ya na shan iska ya na jiran a kawo masa rahotonnin da aka daddatse, aka cire wuraren da su ka kamata ya ji ba.”
Tambuwal kuma ya ce kada a zaɓi duk wanda aka san ya na fama da wata rashin lafiya wadda ya same ta ne saboda yawancin shekaru.
Discussion about this post